Main menu

Pages

ILLOLIN DA MATA MASU SHAN SHISHA ZASU IYA FUSKANTA

 



Barazana da illon da masu Shan shisha zasu iya fuskanta ta fannin kiwon Lafiya, Musamman ma Mata

Akwai wasu jerin illolin kiwon lafiya da mata masu shan shisha ke  samu, wadanda kuma ke shafar jarirai na ciki da kananan yara, a cewar likitoci. 




Wasu daga cikin illolin da ke shafar ‘yan mata sun hada da karancin iskar oxygen a huhu da sankarar huhu da bugun zuciya da ciwon suga da kuma ciwon sankarar bakin mahaifa idan mace ta girma.




Haka kuma hayakin tabar na janyo matsalolin da suka shafi hanyoyin iska da cutar nimoniya ga yara kananan da iyayensu ke shan tabar a inda yara suke.





Ga mata masu ciki kuma masu shan shisha suna fuskantar hatsarin yin bari ko haihuwar bakwaini, ko yara masu jikkatar halitta ko marasa nauyi a lokacin haihuwa da sauransu.





Sai dai a cewar hukumar yaki da cututtuka ta Amurka, CDC, ana iya daina shan shisha ko kuma taba ko da ta zama jiki, ko kuma an yi yukurin dainawa a baya, amma ba a samu nasara ba 




Daya daga cikin muhimman matakan da hukumar ta ce mai son daina shan shishar zai iya dauka shi ne, kudurce wani babban dalili na daina shan tabar.

Comments