Irin Abincin da ya kamata Mai Jego takeci don gyaran jikin ta ciki da waje
Akwai abunda akeso me jego ta gane shine matsewar gaba da cikowarsa wannan kuwa ba kowacce mace ke haifuwa gabanta yake gyaruwa dai yanda akeso ba kuma duk da rashin gyaruwansa kalubalene babba.
.
(1) zaki dafa ganyen zogale tareda albasa sannan saiki tace ruwan ki yanyanka albasan akan zogalen sai kuma ki yanyanka tumatir da cocumber da karas ki saka yajin kuli da maggi kici wannan kwado ya zama duk bayan kwana uku zakici kodai asati sau biyu kafin ace kinyi arba,in gabanki zai ciko ya cika da ni,ima.
(2) idan kina da hali ga naman rakumi wanda anaso shima me jego ko sau daya ne tayi.
Yanda zakiyi shine idan kika wanke namam rakumin saiki dora akan wuta kizuba kanunfari da citta bayan naman ya dafu sosai to wannan ruwan zai kare saiki samu wadannan kayan hadin wato:
- Minanas
- Malmo
- Gurunga
- Gagai
- Girfa
- Habbabah
- Garin Ridi
saiki saka man ayu kadan sannan ki yanyanka farar albasa to anaso kada ki kara ruwa saiki zuba nonon rakumi ya zama shine romon naman kamar dai yanda akeyi da kazar amarya to saiki mayar dashi kan wuta kici gaba da bashi wuta kina juyawa har naman yayi laushi sosai tofa kin gama kizauna ki cinye kisha mamakin cikowar gaba da matsewa tareda ni,ima.
.
(3) Ba abunda ke gyara jiki Mace in ba kayan itaceba fruit ba, saikuma cin danyen tomatir da cucumber kina cinsu inkin yanka, sai kuma zogale ki markada kina shansa da madarar luna sai ki kiyaye shiga rana sannan ki tafasa ruwan kaninfari da xuma kina sha yana saukar da ni’ima ga gyara fata…
Comments
Post a Comment