Ladubba Talatin na karbar addu'a
Matakin farko shine mutum ya zama mai tsarkin zuciya kuma mai ƙoƙarin nisantar shirka da ALLAH.
Kamar zuwa wajen malaman tsubbu, boka da masu bugun ƙasa ko masuyin istikhara wa mutane sauransu.
1• Yin imani da ALLAH ne kaɗai ke biyan buƙatar bayinsa kuma shinr ke amsa kiran bawansa kuma ya biya masa buƙatarsa.
Da kuma yiwa ALLAH biyayya da barin saɓa masa.
[Suratul Baƙarah ayata 186 ]
2• Yin addu'a da Ikhlas, kuma kada ka roƙi kowa sai ALLAH shi kaɗai a lokacin addu'arka da kuma sauran ibadu gaba daya.
[Suratul Bayyinah ayata 5].
3• Yin roƙon ALLAH da Sunayansa maɗaukaka.
[ Suratul A’araf ]
4• Mai addu'a ya fara da yabon ALLAH da girmama shi da yiwa ALLAH kirari, sannan ka roƙi abinda kake buƙata.
5• Sannan kayi salati ga Manzon ALLAH {s.a.w} domin duk addu'ar da babu salatin Annabi {s.a.w} a cikinta, ba’a buɗe mata ƙofofin sama.
6• Fuskantar alƙibla a lokacin yin addu'ar.
[Sahih Muslim]
7• Ɗaga hannuwa a lokacin yin addu'a.
Amma ba'a shafewa a fuska ko a jiki domin Hadisin da yake bayani akan shafar fuska bayan angama addu'a bai tabbata daga Annabi {s.a.w} ba, Idan ka gama addu'a sai ka sauke hannunka wannan shine ya tabbata daga manzon ALLAH {s.a.w}.
8• Ka riƙi ALLAH da cikin hannunka.
Ma’ana ka buɗe hannayan ka cikinsu kana kallon sama.
9• Ka riƙa samun yaƙini akan ALLAH yana amsa addu'arka.
10• Yawaita roƙon ALLAH a kowane lokaci sannan kada ayi gaggawa acikin Addu'a.
[Bukhari da Muslim]
Ma'ana kada kace yanzu-yanzu kake so kaga sakamako, kai dai kayi addu'a kuma kabarwa ALLAH zaɓi.
11• Halarto da hankalinka a lokacin addu'a da ƙoƙarin halarto ma'anonin abinda kake faɗi a yayin roƙon ALLAH.
12• Yin kwaɗayi da fargaba da ƙanƙantar da kai ga ALLAH a lokacin yin Addu'a.
[Suratul A’araf ayata 55]
13• Maimaita addua sau uku alokacin yinta.
[Bukhari da Muslim]
14• Nisantar cin haram da ƙoƙarin yin rayuwa acikin halal.
15• Ɓoye sauti a lokacin addu'a domin addu'a sirrice tsakanin bawa da ALLAH.
Ma'ana: Idan bawa zai roƙi ALLAH anaso ya halarto da abubuwa guda shida 6 a ransa:
• ALLAH ne kaɗai ake roƙo.
• Shi kaɗai yake biyan buƙata
• Shi kaɗai ne mawadaci, kowa faƙirine a wajansa ake nema.
• Idan ya hanaka babu mai baka•
• Yana da ikon ya baka.
• Roƙonsa dolene.
16• Yin addu'a alokacin da kaji kukan zakarah, domin a wannan lokacin mala'ikun Rahma suna kusa.
17• Yin addu'a ayayin da ladan ya gama kiran sallah, har izuwa a tada sallah, da yin addu'a bayan iƙama kafin kabbara sallah.
18• Yin addu'a abayan sallar Nafila.
19• yin addu'a a cikin sujjadar sallar farillah ko ta nafilah.
20• Saka iyaye suyi maka addu'a, musammam uwa.
21• Saka ƙananan yara suyi maka addu'a ko ka rinƙayi suna cewa Ameen, domin ALLAH yana amsa addu'arsu da gaggawa saboda su basu fara aikata zunubi ba.
22• Yin sadaka kafin addu'a ko bayanta yana taimakawa wajen karɓar addu'a.
23• Yin addu'a acikin dare, lokacin da kowa yake bacci, Domin ALLAH TA'ALAH yana sakkowa yana cewa: ina mai neman arzuƙi ya roƙeni na amsa masa, ina mai neman rahma ta ya roƙe ni na amsa masa kamar yadda yazo a hadithi.
24• Tawassili da wani aiki mai kyau da bawa yayi domin neman yardar ALLAH sai ka roƙi ALLAH kayi tawassili da wannan aiki, kamar yadda yazo a hadithi.
25• Addu'a acikin halin tafiya.
26• Addu'a a yayi shan ruwa ga wanda yayi azumi na farillah ko na nafila.
27• Yin addu'a bayan gama karatun Alƙur'ani.
28• Yiwa wani addu'a a bayan idonsa kaima mala'iku zasu roƙa maka irin abinda ka roƙawa ɗan uwanka.
29• Addu'ar mai tsananin biyayya ga iyayensa, shima ana amsa masa da gaggawa.
30• Addu'ar wanda aka zalunta, amma da zai raƙowa wanda ya zalunceshi gafara da shima ya sami sakamako mai kyau anan.
Waɗannan sune kaɗan daga cikin ladubba na addu'a wanda insha ALLAH duk wanda ya kiyayesu ALLAH zai amsa masa addu'arsa da gaggawa.
ALLAH ka amsa mana addu'o'inmu baki ɗaya.
Ameen ya ALLAH.
Comments
Post a Comment