Main menu

Pages

MASHA ALLAH, JARUMA HALIMA ATETE TA KUSA AMARCEWA

 



Masha Allah Alhmdlillh, Fitacciyar Jarumar Hausa film Halima Atete ta kusa shiga dakin Aure.

Ayyirri masha Allah wannan abun yayi mana matukar sha’awa farin cikinmu shine Allah ya baiwa duk 'ya mace miji nagari tayi aure, a Masana’atar Kannywood kuma sai dauka ake daya bayan daya wannan tabbas duk cikarki ‘ya mace gidan miji yafi miki martaba da kima da daraja a nan duniya da lahira.





Majiyarmu ta samu wannan rahoto katin gayyatar auren jaruma halima Yusuf daga shafin sada zumunta Kannywood Exclusive




AURE MARTABA

Fitacciyar Jarumar Finafinan Hausa Halima Yusuf Atete, tana dab da zama Amarya nan da kwanaki kalillan.





Za a daura auren Jarumar ne, da Angonta Mohammed Mohammed Kala, a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba 2022, da misalin karfe 10:30am na safe, a Abuja Sheraton Bus Stop, Juma’at Mosque, a garin Maiduguri, da ke Jihar Borno.





Kafin ranar daurin auren za a yi shagulgulan biki, da suka hada da Kwallon Kafa, Margi Day, Arabian Night, da kuma Dinner


Allah Ya sa Albarka a Auren Ya bada zaman Lafiya Mai dorewa Ameen.


Comments