Shawarwari guda Arba'in Zuwa ga Matar farko wato Uwargida
1.kalmar uwargida ita ce macen farko wanda aka fara aura,duk wacce zata zo sai dai ta shigo ata biyu ko uku harma ta hudu, amma wannan uwargidan ke ce macen farko.
2 .A matsayin ki na uwargida ke zaki fara gina tubalin rayuwar auran ki,ke ce zaki fara tsara yadda zaman ku zai kasance tare da mijin naki saboda da yawa matar farko ita ce makarantan farko ga rayuwar namiji.
3. Ki kula da ibada domin shine toshen komai,ibada dajin tsoron Ubangiji ki san cewa dukkan abinda zaki yi koda a boye ne,idan kin boyewa mijin ki lallai baki isa ki boyewa Ubangiji ba.
4.hakuri da kawaici dole ne ki zama hakan domin zaman rayuwar aure bangaren hakuri shine babban jigo a cikin aure, idan baki da hakuri komai zaina faruwa shiyasa ake son uwargida ki zama mai hakuri.
5. Ladabi da biyayya matukar baki da wannan,tsaf mijin ki zaki fita daga zuciyar sa,kisan cewa mijin ki shugaba ne a gare ki ki masa ladabi da biyayya, matukar abinda ya umurce ki bai kauce wa Addini ba.
6 karki mallaki mijin ki ta hanyar sihiri,zaki hallaka kuma ranan gobe kiyama wuta ta zama makomar ki.
7. Karki je gun wani boka domin neman biyan bukata,idan baki gane kan mijin ki ba,ki Hana idon ki barci ki kaiwa Ubangiji kukan ki cikin dare zaki ga dukkan al'amuran ki sun warware miki.
8. Ki kula da tsaftar jinkin,gidan ki,yaran ki,mijin ki.domin tsabta abu ce mai kyau kuma yana daga cikin musulinci,idan kika zama kazamar mace ke da wulakanci bibbiyu Zaki fuskanta.
9. Iya girki yana daga cikin makamin dake sace zuciyar namiji,idan kika iya girki zaki mallaki mijin ki koma kin wuce raini a wajan sa.
10. Iyayen mijin ki,ki kula dasu ki basu girman su,ki kyautata masu koda kin lura da mijin ki baida niyyan masu abu,ke kiyi amfani da damar ki ki saka ya masu abu,zaki iya masu kyauta daidai karfin ki,ki faranta masu koda ba waje daya kuke dasu ba, saboda sun gama miki komai da suka haifi abinda kika aura.
11. Ki iya zama da dangin mijin ki lafiya,idan sunzo wajan ki ki kula dasu,idan wani abu ya faru kije masu idan na murna ne ki tayasu,idan kuma na bakin ciki ne shima ki tayasu ki zauna dasu lafiya.
12.karki zama wata ballagazar mace marar sanin mutuncin kanta.
13.duk rintse kina kulawa da gyaran jikin ki bawai ko wane irin takarkace zaki na amfani dashi gun gyaran jiki ba,idan baki kula ba da hakan sai ya zama miki matsala anan gaba,ki sani karki na bari mijinki yana jin wani wari a jikin ki,ki kula ta wannan bangaren da kyau.
14. Ki zama mace wanda ta iya ado da kwalliya .
15.duk bayan sati biyu ko kwana goma kije kina yin kitson ki mai kyau,ki lura da abinda mijin ki yafi so,wani nason ganin matarsa da kitso,wani kuma yafi son ganin gashin ta haka a gyare.
16.karki zama mai munanan lafuza ga mijin ki, uwargida kisan irin lafuzan dazaki na amfani dashi gun magana da mijin ki.
17.ko kisan cewa uwargida maza suna son macen data iya kalamai mai dadi? Saboda haka kema ki iya idan ma baki iya ba,ki koya ga zamanin Social media musamman groups din mata ana wayar da kai ki tambaya za'a Koya miki.
18. Ki yawaita yiwa mijin ki addu'a a bayyane dana boye.
19. Ki kyautata wa mijin ki kyakkyawan zato a dukkan al'amuran sa.
20. Ki yawaita tura masa text din soyayya,kina fada masa yadda kike son sa, uwargida karki ce aina daina abinda tun ina budurwa muke yi to yanzu bazan yi ba, lallai kima cire wannan tunanin a zuciyarki, saboda yanzu ne da kukayi aure shine lokacin soyayya.
21.iya shagwaba maza nason mace mai shagwaba kuma suna son ana masu, saboda hakan uwargida ki iya shagwaba.
22. Wani lokacin ki samu irin labari mai abin dariya kina basa musamman idan kika lura da yanayin mijin naki yana cikin damuwa,to kiyi kokarin ganin kin masa maganin wannan damuwar tasa, saboda akwai wasu a lokacin da mutum yake cikin bacin rai a lokacin mace take kara b'ata masa rai, uwargida karki zama daga cikin wannan matan.
23. Ki zama mace mai tausayawa mijin ki don Allah uwargida idan kin kawo masa wata bukatar ki,idan bashi da halin karki daga masa hankali ki masa addua,idan ya samu sai ya miki.
Za a cigaba Insha Allah.
Comments
Post a Comment