Hotunan sabbin kudin da Shugaba Buhari ya qaddamar a jiya da ranar da za a fara amfani da su
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabbin takardun kudaɗen naira a ranar Laraba, a Abuja babban birnin ƙasar.
Kuɗaɗen da aka ƙaddamar ɗin sun haɗa da takardun N200 mai launin ja da N500 mai launin kore da kuma N1,000 mai launin ruwan toka.
An ƙaddamar da kuɗaɗen ne a wajen taron mako-mako da ake yi a fadar shugaban ƙasar a Abuja.
Shugaba Buhari ya ce sababbin takardun kuɗin za su taimaka wa Najeriya ta wajen warware matsaloli da dama da suke addabar ƙasar.
Shugaba Buhari ya ce sauya fasalin kudaden zai yi tasiri ƙwarai wajen taimaka wa ƙasar ta magance matsalar yaɗuwar kuɗi ba bisa ƙai’da ba da cin hanci.
Ya ƙara da cewa sauya sabbin kudaden za su inganta tatalin arzikin Najeriya da ƙara wa kuɗin ƙasar daraja.
Hukumomi a Najeriya sun ce za a fara kashewa ko kuma amfani da sabbin takardun nairar nan take.
"Tsarin da aka aminta da shi a matakin kasa da kasa ya bukaci manyan bankuna da hukumomin kasashe da su rika buga sabbin kudi kowadanne shekaru biyar zuwa takwas.
"Amma yanzu kusan shekaru 20 ke nan da muka sauya takardun kudin kasarmu. Wannan ya nuna tun tuni ya kamata a ce takardar Naira ta samu sabon launi,” ya ce.
Shugaban kasar ya kuma ce sauya fasalin kudin zai taimaka wa tsare-tsaren manufofin kudi na CBN, sanan kasancewar wannan ne karo na farko da aka buga naira a Ma’aikatar Buga Kudi ta Najeriya zai hana yaɗuwar jabun kuɗin.
Shugaban Haka ya ce ko baya ga hakan akwai wasu dalilai na sauya fasalin kudin kasar:
“Akan Sauya fasalin kudi lokaci-lokaci saboda da manufofi kamar haka; inganta sahihancin kudin, da rage yiwuwar buga na jabu, da kare martabar kasa, da kayyade yawan kudin da ke zagayawa, kuma rage yawan kudin ake kashewa wajen tattali da kula da takardun kudin.
"Akwai bukata ta gaggawa ta kayyade yawan kudin da ke hannu jama’a da kuma magance matsalar boye takardun Naira ba a bankuna ba.”
Tun farko CBN ya ce sai a ranar 15 ga watan Disamba ne zai fito da kuɗin da aka sauya wa fasali kafin ya sauya shawarar yin hakan a yau.
A wajen bikin ƙaddamarwar har da Gwamnan CBN Godwin Emefiele da Shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa, da sauran manyan jami'an gwamnati.
Amfanin sauyin hudu
1. Zai taimaka wajen rage tashin farashin kaya domin zai sa a fito da tsoffin kudin da aka bobboye.
2. Zai kuma taimaka waje tsara manufofin da suka jibanci kudi domin za mu samu sahihan alkaluma kan yawan kudin da ke akwai.
3. Sabon tsari zai taimaka wajen shigo da kowa cikin harkokin kuɗi da rage yawan hada-hadar kuɗi laƙadan da kuma tabbatar da cewa Najeriya ta bi sahun tarin hada-hadar kuɗi a zamanance.
4. Sauya fasalin kudin kuma zai taimaka wajen yaki da almundahana domin hakan zai sa a yi ta kokarin dawo da manyan takardun kudi wadanda su ne ake amfani da su wajen almudahana kuma hukumomin tsaro za su iya gani idan ana kokarin fitar da irin wadannan kudaden daga bankuna
A watan Oktoban da ya gabata ne Babban Bankin Najeriya CBN, ya sanar da matakin sauya fasalin kuɗaɗen ƙasar, tare da umartar mutane da su mayar da tsofaffin kudaɗen banki don sauya musu da sababbi.
CBN, ya ce idan mutane suka mayar da kudaden ba tare da bata lokaci ba, to za su iya samun musayar kudinsu a kan kari.
Ya ce saboda wannan sabon tsarin yanzu an cire duk wani caji da ake yi a kan kudin da ake kai wa bankuna ba tare da bata lokaci ba, kuma duk yawan kudin.
Comments
Post a Comment