Tarin sunadarai da Ganyen Mangwaro ya kunsa da amfanin da yake a jiki
Ganyen Mangwaro ya kunshi sunadarai masu tasirin gaske ga lafiyar dan Adam wajen kawar da wasu cututtuka da suka saba addabar al’ummar musamman a wannan zamani. Ire-iren wannan sunadarai sun hada da:
- Alkaloids
- Phenols
- Flavonoids
- Saponins
- Tannins
- Calcium
- Magnesium
- Potassium
- Phosphorus
- Sodium
- Copper
- Zinc
- Cadmium
- Ascorbic acid
- Riboflavin
- Niacin
- Thiamine
A sakamakon wannan arziki na sinadarai da Allah yayiwa ganyen mangwaro Yana maganin wadannan cututtukan:
1- Ciwon Sugar
Ganyen mangoro yana daidai ta suga, sabida yana dauke da sinadarai masu saka jiki ya saki insulin.
Ana iya jika ganyen magwaro a cikin ruwa ya kwana sai ayi amafani da shi yana taimaka wajen daidaita suga.
Haka Kuma za'a iya barin sa ya bushe sannan a maida shi gari adinga amfani dashi domin daidai ta suga.
2- Hawan Jini
Kasancewar ganyar mangiro yana dauke da sinadaran vitamin hakan zaisa ya kona cholesterol mara amfani a jikin mutum, sannan ya daidai ta jinin mutum.
3. Matsalar Koda
Ana dafa ganyan mangoro kamar shayi a dinga sha da safe a matsayin abincin farko yana kawar da matsalar Koda, kuma yana narkar da tsakuwar koda tare da tsarkake ta daga cututtuka.
4- Matsalar Kirji; (Respiratory Track Infection)
Ana iya dafa ganyan mangoro kamar shayi sannan a saka zuma a ciki ana amfani da shi ya saukake matsalar tari da rike kirji.
5- Cutar Atini
Akan sha garin ganyen Mangwaro da aka jika da ruwa wajen samun waraka daga cutar atini ko da kuwa mai zuwa ce da fitar jini.
Comments
Post a Comment