Yadda Ake Kayyade haihuwa (family planning) da Kanumfari, Garafunu da Kuma Zurman.
Akwai Abu uku da suka shahara a maganin gargajiya me dakatarda daukan ciki, wadannan abubuwan kuwa sune;
- Kanunfari (cloves)
- Garafunu (cerasee)
- Zurman (ricinus communis)
Ana iya aiki dasu duka lokaci daya wato a hadiyi 'ya'yan zurman guda daya a mako daya sannan a tafasa ruwan kanunfari da yayan garafunu ana shan sa kullum a mayar dashi ruwan sha, wannan kuma anayine a daidai lokacin da mace ke kusa da mijinta wato miji Yana saduwa da ita.
Sannan ana iyayin kowanne daban wato ko zurman kadai ko kanunfari ko kuma garafunu kadai,
Wadannan ana yinsu cikin sauki su hana mace ta samu ciki,
To Amma abunda ba kowa yake tsayawa ya fahimta ba shine zuwa yaushe za asamu ciki?
ko kuma daga mace ta daina shikenan?
To a bincike da akayi wadannan duka suna Hana maniyin namiji Shiga mahaifane ma'ana sukan juyarda akalarsa bazai Shiga mahaifaba,
To saidai fa kowanne lokaci aka sadu da mace ba lallai manayin namiji yabi fitsari ya fitaba wani yakan Zama Yana sakata ciwon mara, wasu kuma hakan Yana kawo ciwon sanyi me saka ciwon mara,
Sannan kuma koda mace ta daina ba lallai ciki ya samu da wuriba don idan bakin mahaifa bai daidaitaba maniyin bazai taba shigaba ballantana ciki ya samu,
Amma hakan bazai Zama matsala ga mace ba Insha Allah.
Comments
Post a Comment