Main menu

Pages

YADDA AKE HADA KALOLIN CURRY CIKIN SAUKI A GIDA

 



Kalolin curry da yadda Ake Hadawa a gida cikin sauki

Curry, wani nau’i ne na daga cikin abinci da muke amfani da shi, kuma a cikin abincin wadannan ganyaye firanni da tsurirrika hade da saiwoyi duk su ne idan aka hada su ake samun curry, kuma dukkansu; daya bayan daya suna dauke da sinadarai masu kara karfi; wato “carbohydrate”, Karin lafiya, garkuwar jiki walwala, protein, da vitamins, tare da kuma mataki ko wane a tattare. Sannan kuma magunguna ne musamman masu nasaba da sanyi, kumburi tari, kunne, hakori, hanci, da dai sauransu. Don haka, curry yana fitowa ta hanyoyi daban-daban kamar a matsayin kanshi a abinci, kala, magani, duk a cikin abinci a lokaci daya





Abubuwan da ake hada curry da su:

Yansun gw 4, siitur 4 gwn, kamun gwn 4 shamar gwn 6, hulba gw 1, Bakin algarif ¼ , Tafarnuwa, gw 1/6, Citta mai yatsu gw5, yari gw2, Kurkum gw6, Kusbara gw2, kanunfari gw1/6, Jawa gw1/6, Masoro gw ½, Kimba.





Yadda ake Curry

Za’a hada duk wadannan tserrai, da firanni da saiwoyi a gyara, a tsabtace su, a nika su, su yi laushi sosai, zai ba da ingataccen curry. Idan bai laushi sosai ba za a iya tankadewa.





Rabe-Raben curry

Curry ya rabu kala daban-daban kamar a yi wasu hade-hade na kayan kanshi, na canzawar kalar shi da kuma dandanon shi.





1. Za’a hada duk wadannan tserrai, da firanni da saiwoyi a gyara, a tsabtace su, a nika su, su yi laushi sosai, zai ba da ingataccen curry. Idan bai laushi sosai ba za a iya tankadewa.


2. Idan an hada gyadar miya (wato ‘yar sokoto ) da citta mai yatsu zai bada ingataccen launin na kayan kanshi wani kala daban.


3. Kanin fari, masoro da citta mai ‘ya’ya suma wasu launi ne na kayan kashin.


4. Shamar, yansun suitor idan aka hada su zai bada wani launin kanshi a abinci ko a miya.


5. Haka kuma ko wannen su aka dauka zai bada dandano da za’a gamsu da shi.

Comments