Main menu

Pages

YADDA MACE ZATA KIYAYE KAMUWA DA BREAST CANCER

 



Sharhi akan abinda ke kawo breast Cancer, da yadda za a kiyaye faruwan hakan

Na sha jin mata a wajen hira a gidajen biki ko a tattaunawar zaurukan WhatsApp suna magana a kan amfani da rigar nono, wato bireziya mai datti na iya jawo kansar mama.


A wasu lokutan kuma sai na ji ana cewa ai har saka bireziya mai irin karfen a jiki dinnan ko wacce ta matse mace sosai na iya jawo kansar.




Zantukan sun sha ba ni mamaki ganin yadda kai tsaye matan ke fadar hakan, idan aka tambaye su a ina suka ji da wuya su iya fada.


Su a ganinsu kawai dattin bireziya da karfen da ke jikinta da kuma matse mutum fa za ta yi sosai sun isa sanadin kawo kansar nono.




Shin haka din ne da gaske? Akwai wani bincike na kimiyya da ya tabbatar hakan na faruwa?

Za mu duba amsoshin wadannan tambayoyi a cikin wannan makala ta hanyar tuntubar likitoci. Wannan makala mun rubuta ta ne albarkacin watan wayar da kai kan sankrara mama, da ake yi a cikin duk watan Oktoba a fadin duniya.


Dr Hannatu Ayuba kwararriyar likitar kansa ce a babban asibitin kasa da ke Abuja, wato National Hospital, kuma a jawabin da ta yi wa BBC Hausa ta ce cutar kansar mama ba ta da wata alaka da bireziyar da mata ke sakawa. "A gaskiya ba wani bincike na kimiyya a fadin duniya da ya taba cewa saka bireziya mai datti ko mai karfe ko matsattsiya na jawo cutar kansar mama.




"Wannan wani camfi ne kawai da ba mu san daga inda ya fito ba," ta fada.


Sai dai duk da haka likitar ta jaddada muhimmancin sa bireziya tsaftatacciya kuma wacce ba ta matsi mace ba.


"Ya dai kamata mata su san cewa ita tsafta aba ce mai kyau, ko da bireziya mai datti ba ta jawo kansar mama ya kamata mace ta san cewa tsafta na da muhimmanci.


"Bai kamata a shafe kwanaki ana saka bireziya daya ba tare da wanketa ba.


Sannan a daya hannun bai kamata a dinga saka bireziya matsattsiya ba, don tana hana mutum sakewa," a cewar Dr Hannatu.




Me ke jawo kansar mama?

Likitoci a fadin duniya sun yi ittifakin cewa kansar nono ita ce mafi muni da saurin kisa fiye da dukkan sauran nau'ukan kansa.Ga dai wasu daga cikin abubuwan da ke jawo ta.

- Gado daga iyaye ko dangi na kusa

- Shan taba sigari da barasa


- Rashin motsi jiki Gurbacewar muhalli wato kamar gurɓatacciyar iskar shaƙa da ruwa da ƙasar noma




Alamomin kansar mama

• Babbar alama ta kansar mama ita ce ɓullar ƙurji a jikin maman wanda a da babu shi. 


•Idan girman maman ya sauya ta hanyar raguwa ko ƙaruwa, ga mama ɗaya ko duka biyun


• Idan wani ruwa yana fita daga kan maman • Idan kaluluwa ta fito ƙasan hammatar mace


• Idan wani ɓangare na maman ya ɗan loɓa ciki 

• Idan aka ga wasu ƙuraje sun fito a kan maman


• Idan kika ga wani sauyi kan nonon, ko kuma kan nonon ya fara lumewa ciki. 


• Sai dai masana lafiya sun ce ba kowane ciwon nono ne yake zama alamar kansar mama ba.

Comments