Amfanin Na'a Na'a da manta ga Lafiyar jikin Dan Adam
Na'a Na'a ko Kuma Mint A Turance an san amfaninsa tun kusan zamanin Kunne ya girmi kaka. Romawa Sun Kasance suna amfani dashi a matsayin abin Sanyawa a Ruwan wanka (domin samun lafiyayyar fata), haka kuma sun kasance suna yin girki dashi.
Rumawa a wancen lokaci sun kasance suna kiran Na'a Na'a da Mentha, Mentha a Yaren Girkanci ana nufin Magani. Shiyasa suke amfani da shi a wajen Maganin Mura, Gyanda, tare da warkar da Ciwukkan da suka shafi fatar Jiki. muke gabatar muku da amfanin Na'a Na'a Kama daga ganyensa har ya zuwa Man Sa.
In shaa Allahu a Wannan Karon Ma zamu gabatar muku da Wasu daga cikin amfanin Na'a Na'a. Amfani da Na'a Na'a na hana fitowar kurajen fuska idan kuma ya riga ya fito sai a rika shafa man za'a samu sauki musamman ga masu maikon fuska.
Shafa danyen ganyen Na'a Na'a aka na maganin ciwon kai haka kuma idan ana goge hakora da bushashshen shi yana sanya hakora su yi haske. Ganyan Na'a Na'a Na Tsuke Macce (zamuyi bayaninsa daga baya In shaa Allahu). Yawan Shan Na'a Na'a nasa baki ya rika kamshi koda yaushe shi ya sa rumawa a wancen lokaci idan sun ci wani abu mai sanya warin baki kamar albasa ko tafarnuwa su kan wanke bakin su da na’a-na’a.
Yin hayaki da busashshen na’a-na’a ayi turare da shi yana sanya kamshin jiki da kuma kanshi ga wurin da aka yi turaren haka kuma idan aka shaki kamshin da hayakin yana maganin mura. Ana hada na’a-na’a da zuma a rika sha domin samun karfin jiki kuma yakansa nishadi da samun lafiyar hanta ta rika aiki da kyau da kawar da mura da narkar da abinci da karfafa zuciya ya zamanto cikin koshin lafiya koda yaushe da kuma kumburin ciki.
Ga wanda yake fama da rashin jin dadi kamar wata matsala na damunshi ana hada shayin Na'a na'a yasha na sha Insha Allahu za a rabu da matsalar. Matsalar daukan ciki ga mata masu juna biyu kamar masu yin amai ko yawan zubda yawu in sun samu ciki sai su samu ganyen su wanke su rika taunawa ko kuma su sanya a bakinsu.
Comments
Post a Comment