Main menu

Pages

YADDA ZA A HADA SAHIHIN MAGANIN ZAZZABIN TYPHOID KO MALARIA

 



Sahihi Kuma ingantaccen maganin Zazzabin Typhoid/Malaria Insha Allah

Kana fama da yawan zazzaɓi mai zafi wanda bai jin maganin bature, ko kuma mai naci wanda yake tafiya ya dawo? Akwai alamun kana da Cutar Typhoid/Malaria a jikinka. Idan Typhoid ta haɗu da Malaria abun yana yin Worst, in ma kwana ya ƙare har lahira takan kai mutum.





Malam duk ka manta kawai da haɗiɗiyar ANTI MALARIA, akwai wani laƙanin magani wanda kai da kanka zaka haɗa abinka a gida, kuma in Shaa Allahu idan ka yi shi zaka gode wa Allah, domin mujarrabi ne, an gwada ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba. Kuma cikin yardar Allah waraka ta samu.





Abubuwan da kake buƙata:

1. Lemun kwalba (7Up) Kwalba 2.

2. Karan zaƙi (Rake) kamar yankan N50 ya wadatar (ya danganta da araharsa a yankin ku!)

3. Lemon Tsami, kamar guda biyar zuwa takwas.

4. ALABUKUN Sachet powder (1 Sachet)





Yadda zaka haɗa maganin:

1. Ka samu 'yar tukunya ƙarama, sai ka juye lemon kwalban a ciki (LURA: 7Up kaɗai ake amfani dashi).


2. Ka yayyanka karan/raken ƙanana-ƙanana ka zuba cikin tukunyar.


3. Ka yayyanka lemon tsamin rabi-rabi, ka zuba ciki.


4. Sai ka juye sachet ɗin garin ALABUKUN ɗin a ciki.


5. Ka ɗora bisa murhu ka dafa har sai ya tafarfasa kamar na minti goma zuwa sha biyar (LURA: ba a sanya ruwa!)


6. Sai ka sauke ka buɗe ka bar shi ya huce. Sannan sai ka samu rariya da kofi ka tace ka sha rabi. Zuwa can bayan kamar sa'a takwas ka ƙarasa ragowar.





Insha Allahu zaka ga yadda waraka zata zo maka cikin gaugawa, domin an gwada shi ya fi a ƙirga, a duk lokacin da zazzaɓi yayi zafi, da zarar an haɗa wannan laƙani sai a samu lafiya cikin Yardan Allah.





Kai ko lafiyarka ƙalau ka haɗa wannan magani ka sha, sai ka ji yadda jikinka zai ƙara lafiya da kuzari. In so samu ne ma duk wata ka rinƙa yi kana sha. Kuma maganin ga ɗan karan daɗi nake gaya ma, ba a ba yaro mai ƙyuya! 


A yi “sharing” domin amfanin Al'ummar Annabi SAW.

Comments