Main menu

Pages

YADDA ZA A MAGANCE MATSALAR MAFITSARA (BLADDER)

 



 Yanda za a Magance Matsalar Mafitsara (bladder) cikin sauki

Wanda ke fama da matsalar fitsari, wato Yana yinsa a yayyanke sannan ga ciwon bladder. To Abu na farko shine a ziyarci asibiti. Sannan Kuma za a iya gwada yin wannan;

 



1. Ka samu 'Ya'yan Kabewa Cokali bakwai, 'Ya'yan Kankana ma cokali bakwai, 



 2. Ka nika kowanne daban daban. 


3. Ka samu tafasasshen ruwa, ka zuba garin 'ya'yan kabewar nan Cokali guda aciki. 


4. Ka barshi ya huce (ba wai sanyi ba) sannan ka zuba Zuma aciki, sai kasha da safe kafin karyawarka da minti 15. 


5. Da yamma kuma sai kayi ma 'ya'yan Kankanar nan haka. Sannan kasha. Kuma zaka maimaita haka har sati guda. 



Ko Kuma ka hada wannan;

 Ka samo Katuwar Albasa guda daya. Ka yanka gida hudu sannan ka dafata da ruwa kofi guda. Idan ta dahu, ka tace ruwan, Sannan ka zuba Zuma sosai acikinta sannan kasha. 



Insha Allahu wannan zai maka maganin Basur mai kaikayi, ko mai tsiro, ko basur mai Jini, ko ciwon Cancer, ko Ciwon mafitsara, ko Ciwon Qoda, ko tsakuwar Qoda. Allah yasa adace. 



Comments