Main menu

Pages

YADDA ZA A MAGANCE MATSALAR SHANYEWAR BARIN JIKI (PARALYZED)

 



Hanyoyin da za a bi wajen magance Matsalar shanyewar jiki yaro ko babba

  Kasancewar da yawa daga cikin Alumma wannan zamani suna fama da irin wannan matsalar, Ko kuma wasu daga cikin Makusantansu, Shi muka lalubo muku wasu fa'idodi domin a jarraba :


 



   1. Marar lafiyan ya yawaita Shan Nonon rakumi, kuma asamu narkakken 'bargon Qashin Saniya arika sanya masa acikin abincinsa, kuma ana shafa masa adukkan gabobin da suka shanye din.

Wannan fa'idar tana da Muhimmanci ga Qananan yara wadanda wani 'bangaren jikinsu ya shanye, ko kuma jikinsu babu Qarfi.




   2. Asamu Kwaiduwar Qwan Tattabara (Wato yellow din cikin ruwan Kwan). A hada da ruwan albasa, da tafarnuwa. A gauraya arika shan cokali biyu safe da dare. Amma idan Qaramin yaro ne arika bashi cokali daya tak.


Kuma arika shafa man Jimina ajikin Qafa ko hannun da yake ciwon.

Masu fama da shanyewar gabobi, ko kuma rashin Qarfin jiki in sha Allahu zasu samu waraka.





   3. Asamu 'bargon Qafar rakumi (wato na wajen kwabrinsa) a narkar dashi sannan a gaurayashi da Man habbatus Sauda mai kyau


Arika shafa ma marar lafiyan jikin kafadunsa da kuma Qashin bayansa, da kuma gabobin da suke ciwon. In sha Allahu Za'a ga abun mamaki wajen samun waraka da izinin Allah.





    4. Arika dafa tafarnuwa, ana bama marar lafiyan ruwanta yana sha tare da zuma, Kuma ana bashi man tafarnuwa wanda aka hada da bargon saniya. Amma idan za'a narkar da 'bargon ba soyashi za'ayi ba. A rana za'a sanyashi har sai ya narke da kansa wannan faida tasamo asali 


Allah Ya sa a dace Yaba dukkan Musulmi Lafiya Ameen.

Comments