Yadda ya kamata Maza suna kula da Qannensu ko yayyensu Mata
"Da yawan mu muna da ƙanne mata a cikin gidajen mu, kuma da yawan mu ba ma damuwa da halin da suke ciki na ƙuncin abin siyan abinda ya dangance su na sirrin rayuwarsu. Don Allah mu dinga taimaka musu da ɗan kuɗin abin da za su dinga siyan abinda yake na sirrin rayuwarsu ne bawai har sai sun tambaye mu ba, muddin baza mu dinga taimaka musu ba, to haƙiƙa wasu matan raunin zuciya zai same su har takai ga suna kula mazan da za su dinga basu kuɗi suna biyan buƙatun su a kansu, Allah ta'ala ya kiyaye faruwar hakan"
"Kuskure ne babba ace kana da ƴa ko ƙanwa amma kuma baka san ka basu kuɗi ko ka tambaye su abinda suke so ka siyo musu ba, haƙiƙa kunya takan hanasu tambayar ku kuɗi don sinya abin sirrin rayuwarsu"
"Allah kaɗai yasan halin da suke shiga ciki idan a lokacin da suka rasa ɗan kuɗi a hannunsu kuma gasu da buƙatu masu yawan gaske waɗanda kuma suke jin kunyar bayyanar muku dasu"
Comments
Post a Comment