Abubuwan da ke haddasa zubar ruwan Mama ba tare da goyo ko ciki ba, da alamomin da za a gane matsalar
Idan mace ta fahimci Tana ganin ruwa na fita ta mamanta alhali tasan ba ciki ba goyo to a bibiyi ko nazari akan wadannan dalilai.
1- Shan magunguna, Anfani da wasu magunguna kan haifar da zubar ruwan Mama alhali ba ciki ba goyo.
2- Shan magunguna masu sa bacci ko buguwa, magungunan cutar damuwa, Magunguna na kwakwalwa, da magungunan hawan jini duka suna sa ruwan Mama.
3- Opioids, Magungunan karfin jiki rage zogi da ciwon jiki matukar mace na yawan Anfani da wadannan ababen suna sa wannan yanayin.
4- Herbal, Ina mata masu shaye shayen Magungunan zamani na Mata to suna sa wannan yanayin.
5- Magunguna na tazaran haihuwa idan mace na Anfani da magungunan tazara zata iya haduwa da yawan zubar ruwan Mama.
6- Matsaloli na Pituitary, idan mace nada matsala ta pituitary Tumors ko disorder a wannan gland din za a iya haduwa da fitar ruwa ga Mama ba ciki ba goyo.
Da sauran dalilai dake iya haifar da wannan wadanda ban ambata ba.
Ana Anfani da matakin magani ko ma aiki a cire Tumors din, sannan ana takaita Anfani da duk wani Abu dazai Kara prolactin level.
Alamomin da Mace zata fahimci tana da Matsalar fitar Ruwan Nono (Galactorrhea)
- Fitar ruwan a nono kamar Madara alhali ba ciki ba goyo.
- Fitar Ruwan mama masu kauri
- Fitar Ruwa idan mace ta matsa ko aka matsa mamunan Daya ko duka.
- Rashin yin al'ada ko barkacewar al'ada.
- Zazzabi, Ciwon kai dama gani biji biji.
Duka wadannan suna daga cikin alamomin da mace zata gani tayi zargin ko tana da wanann matsalar.
Akwai shawarwari da magungunan daya dace ayi amfani dasu bayan anje anga likita. Mafiya yawa babban abunda yasa ba a samun nasara shine boye gaskyar abunda ya faru ko abunda mace tasan tayi, taki bayani ko gaya ma likita gaskiya.
Musamman amfani da magungunan Hana daukan ciki, Shaye shayen wasu magunguna na daban da sauransu.
Comments
Post a Comment