Yadda farin ciki yasa wata Mata ta hadiyi zuciya ta mutu nan take - Fauziyya D Sulaiman
Fitacciyar mai gidauniyar taimakawa marasa karfi da marayu Fauziyya D suleiman inda ta bada wani labari mai tada hankali inda anka baiwa wata baiwar Allah taima ta fadi da mutu Allahu Akbar ga abinda ya faru nan.
Na yi taimako amma ya zame min tashin hankalin da na kasa aiki yau, daga ba baiwar Allah kudi ta hadiyi zuciya ta mutu.
Na san ba ku manta da wata yarinya da kwanaki rayuwarta ta so lalacewa sakamakon kasa biya mata kudin sauka da mahaifiyarta ta yi wani tsinannen mutum ya so yin amfani da wannan damar ya lalata rayuwarta Allah ya kareta har muka biya mata kudin saukar.
Daga nan muka fahimci gwara mu aurar da yarinyar nan tunda shekararta bata wuce 16 ba bata da wayo, mahaifiyarta ta ce ba zata iya yi mata aure ba, saboda daman ita ce ke wahalar yawon aikatau ta ke ciyar da marayun yaranta wanda su bakwai ne, da kyar ta ke iya samun dari biyar a rana ta ciyar da su, shi ya sa ma ta kasa biyan kudin saukar tsahon shekaru uku, hatta gurin zama gagarta ya yi sai da aka taimaka mata aka bata aron guri, sai muka ce kar ta damu a group din mu na SADAKATULJARIYA za mu hada kudi mu yiwa yar ta aure insha Allah don haka aka saka rana.
Tsahon watanni muna tara kudinnan, jiya na turawa wakiliyarmu kudin da nuka tara a sai mata kayayyaki daidai na talaka saboda gobe asabar zaa daura auren.
Ana kai kudinnan matar nan ta kalli kudin ta fashe da kuka da murna, tana magana cikin kuka tana cewa wanne irin mutanene wadannan, yanzu daman yarta za ta yi aure ta samu wannan gatan, daman za ta ga auran yar ta, wacece wannan Fauziyyan, ta dinga addua kala-kala sai ta durkusa ta na godiya ga Allah daga sannan ba ta motsa ba.
Wakiliyarmu da ta ji shuru ta taba ta ji babu mumfashi ta kira jamaa aka dauketa aka yi asibiti, yanzu dai baiwar Allah nan ta rasu saboda tsananin farin ciki.
Ta rasu tabar yaranta guda bakwai da Allah ne gatansu itace gatansu, sai ta futa ta yi aikatau ta ke ciyar da su, gobe ne ta kamata a daura auran yar ta amma ba zata gani ba, abun da ta jima tana jira, Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun
Na jima banga tashin hankali irin wannan ba, kudin da ta gani su suka gigita baiwar Allah nan, wallahi marayu suna cikin tashin hankali, baa taimaka musu a inda suke sai kalilan da suka dubi Allah, jamaa don Allah ku dinga taimakawa marayu da iyayansu, Allah ka duba yarannan.
Ga Karin bayani daga Bakin ta
Comments
Post a Comment