Amfanin Ambar guda Sha shida (16) ga Lafiyar Dan Adam da Kuma Miski, da yadda za ayi amfani dasu
Ambar wani magani ne da ake samun sa daga jikin wata bishiya. Wato kamar irin farin ruwan nan dake fita daga jikin bishiya. Shi ne ake haɗa shi da wasu sinadarai a samar da Ambar. Kuma ana samunsa a jikin bishiyoyi da dama. Idan ku ka duba wannan hoton za ku ga hoton Ambar kamar ƙaro.
Bayan amfanin da Ambar yake da shi wajen kiwon lafiya, haka ma yana taimakawa wajen magance cututtukan jiki da na jinnu ko sihiri.
Ana iya haɗa Ambar da wasu magunguna kamar zuma, miski, habba, zaitun, da dai sauransu, ayi amfani da shi don samun ingantacciyar lafiya
Yi amfani da Ambar kaɗan ka samu lafiya mai yawa da yardar Allah.
Ana samun Ambar na gari, ana samun na ruwa, ana samun na turare, ana samun kwaɓaɓɓe na shafawa .
- Sanya nishaɗi.
Ambar yana sanya nishaɗi idan aka sha kilogram ɗaya tare da zuma cokali ɗaya.
- Ƙara ƙarfin haƙora.
Ambar yana ƙara ƙarfin haƙori idan ana goge haƙora da man sa, wato Amber oil.
- Gyara ƙwaƙwalwa.
Man Ambar yana maganin cututtukan ƙwaƙwalwa idan ana shan sa tare da Man zaitun
da Habbatussaudaa.
- Maganin ciwon Hauka.
Ga mai lalurar hauka sai adinga tofa ayoyin Ruq'yah a cikin Ambar, a zuba a ruwa, a ba shi, ya sha kuma a dinga yi masa hayaki da shi musamman ahaɗa da miski wajen hayaƙin.
- Ciwon kai.
Ciwon kai ɓari guda sai a haɗa Ambar da jan miski da Man juda a kwaɓa, a dinga shafawa a kan kuma ana yin hayaƙin sa.
Lalata sihiri.
Ana amfani da Ambar ta hanyoyi da dama wajen ɓata sihiri wanda mutum ya ci ko ya sha.
- Hawan jini.
Masu hawan jini su sha Ambar kaɗan a cikin ruwa.
- Gyaran fata.
Don gyaran fata da jin daɗin jiki, sai a diga Ambar kaɗan a cikin ruwan wanka ayi wanka da shi.
Daɗin bacci.
Mai son yin bacci mai daɗi shi ma sai ya zuba Ambar kaɗan a ruwan wankansa.
Hutawar ƙwaƙwalwa.
Ambar yana taimakawa ƙwaƙwalwa wajen samun hutu mai daɗi.
- Lafiyar zuciya.
Amfani da Ambar yana ƙara kyautata ƙarfin zuciya.
- Asthma.
Masu cutar Asthma su ma Ambar yana taimaka musu idan suna amfani da shi.
- Gudanawar jini.
Amfani da Ambar yana ƙara kyautata gudanawar jini a jikin mutum.
- Ƙarfin jima'i.
Yin amfani da Ambar yana kuma ƙara ƙarfin jima'i ga maza da mata.
- Narkewar abinci.
Amfani da Ambar na sauƙaƙa narkewar abinci a cikin ciki, yana hana kumburin ciki, tusa da sauran matsalolin ciki.
- Daɗin jiki.
Yana ƙara soyayya tsakanin miji da mata, idan ɗayan su yana amfani dashi.
- Warkewar ciwo da kashe ƙwayoyin cuta. Sai a zuba man Ambar a kan ciwon bayan a wanke shi. To zai warke cikin sauƙi insha Allah.
Abin Lura
Duk da amfanin Ambar kuma zai iya cutarwa shima
- Mata masu ciki su guji amfani da Ambar, musamman sha a ciki.
- Ambar ɗin da ba a gauraya shi da wani abu ba kamar ruwa da makamantansu, to a guji shan sa kai tsaye.
- Ba'a sa Ambar a cikin ido.
- A guji ajiye Ambar kusa da yara.
Daga cibiyar AL-manar Islamic medicine, masu yin Ruq'yah da harhaɗa Magunguna na Musulunci. Lambar waya 08162417777.
Amfanin Almiski
Shi Miski ba tsiro ba ne, ana samar da shi ne daga jikin Barewa, kuma Allah ya faɗe shi a Alqur‘ani.
- Yana maganin dafi kowanne iri.
- Yana ƙara ƙarfin jiki.
- Yana maganin hawan jini idan an sheƙa a hanci
- Yana maganin Aljanu, ya kan ma iya kashe Aljani idan an haɗa shi da Za‘afaran ana shafawa, ana kuma iya zuba shi a garwashi a dinga hayaƙi.
- Yana maganin warin gaba idan ana shafawa.
- Yana maganin namijin dare.
- Yana taimakawa masu matsalar haihuwa idan suna matsi da shi bayan gama al'ada.
Akwai jan Miski, akwai baki da kuma farin Almiski akwai kuma miski na ruwa.
Comments
Post a Comment