Amfanin cin dafaffen kwai guda Bakwai (7) a jikin Yara da Manya
Ba yara kadai kwai yake ma matukar amfani ba a lokacin tasowarsu, har da manya
- Kwai yana kunshe da sinadarai masu matukar amfani ga lafiyar dan Adam
- Dafaffen kwai na kara karfin kashi a jikin yara kanana don yana dauke da Vitamin D Ga yara kwai a lokacin da suke tasowa na da matukar amfani domin yana inganta girman jikin yaran saboda sinadarorin da kwan ke dauke da shi.
Kwararru sun nuna cewa kwai na dauke da sinadarorin Vitamin A, B12, D, B6 wanda ke taimakawa wajen kara karfin garkuwan jiki yara musamman ‘yan kasa da shekaru 5.
1. Dafaffen kwai na bude kwakwalwan yaro.
2. Dafaffen kwai na dauke da sinadarin ‘lutein’ and ‘zeaxanthin’ wanda ke kara lafiyar idanuwan yaro.
3. Dafaffen kwai na kara karfin kashi a jikin yara kanana domin yana dauke da sinadarin Vitamin D.
4. Dafaffen kwai na dauke da sinadarorin leucine, phenylalanine, histidine, isoleucine, lycine, methionine, threonine, tryptophan da valine wadanda ke taimakawa wajen gina jikin yaro da kuma kara masa jini.
5. Dafaffen kwai na kara girman kunba da gashin kan yara.
6. Omega-3 da ke cikin dafaffen kwai na taimakawa wajen bude kwakwalwar yaro kuma zai yi saurin gane abubuwa.
7. Dafaffen kwai na dauke da sinadarin Iron da ke taimakawa wajen samar da issashen jini a jikin yaro Wanda rashin shi yakan sa aga yaro na kumbura.
Comments
Post a Comment