Main menu

Pages

AMFANIN RUWAN KWAKWA DA MADARAR KWAKWAR GA LAFIYA

 



Amfanin Ruwan kwakawa da madarar kwakwar duka gaba daya da ya kamata ku sani.


Ita dai Kwa-kwa wacce a Turance muka sani da Coconut ta kasance daya daga cikin muhimman tsirran itatuwa masu zama a matsayin abinci da kuma magani na musamman.





Lokuta da dama zaka ga mutum ya shagaltu da cin wani abu na daban da cinsa baya da wani amfani ga jiki kuma ya kasa daina cin wannan abin. Haka kuma zaka tarar mutum na cin wani abu da baima san amfanin cinsa ba amma kuma sai a tarar yana amfanar jikinsa.




Ganin haka yasa na duqufa da zaqulo tsirran itatuwan da Allah yahuwace mana anan kasar Hausa. Tsirran itatuwan dake zama a matsayin abincin dake gina jiki, inganta lafiya da kuma maganin cutukka.




Amfanin Ruwan kwakawa (Coconut Water)

Akan samu ruwan kwa-kwa a lokacin da aka fasa kwakwa sai a  rabata biyu to za a ga wadannan ruwan wadanda Natural Solution ne dake kumshe da irin wasu sinadirai kama daga na  Vitamins

B1, B2, B3, B5, B6, B7, B9, Calcium, potassium Sodium, Vitamin C, da sauransu. 




Daya daga cikin manyan faidodin ruwan kwakwa shi ne saurin maido da karfin jiki a bayan da aka sha wahala na yanayin wani aiki ko jinya ta rashin lafiya.

Za a nemi lita daya ta ruwan kwakwa a rinka kwankwada. Za a ji garau a jiki.





Fa'ida ta biyu - Maza magidanta wani hadine a gareku dake maida karfi bayan saduwa. Domin jima'i yana tafiyar da karfin jiki a dalili da maniyin da ya zuba wanda dauke yake da Sinadiran calcium wadanda sune ke baiwa jiki karfi.




Wannan ne dalilin da yasa namiji kejin karfin jikinsa ya ragu a bayan inzali. Sai a nemi lita daya na ruwan kwakwa a kwankwada bayan an kammala saduwa.




Ruwan kwa-kwa na kara yawan ruwan jiki(increases electrolyte)

Ruwan kwakwa na baiwa jiki kwari da karfi na jiyoji da kassa.

Natural Energy Drink ne da yan kwallo zasu iya amfani dasu dan samun karfi da kuzarin gudu a yayin wasa. Sun fi duk wani kayan sha na kolba dake daukeda extra sugar.




Ruwan kwakwa na tafiyar da gajiya da ciwon jiki bayan fama da wani aiki  na wahala ko doguwar tafiya.


Ana hada ruwan kwakwa da garin Cinnamon (kirfa) sai a kwa6a a sha a sanda za ayi karatu dan samun saurin fahimta da rage damuwa ko yawan tunani.




Mata kan iya amfani da ruwan kwakwa da nonon rakumi amma kadan sai su dama garin ridi dasu sai su rinka sha.

Wannan wani hadine na samun Ni'ima da gamsuwa a yayin saduwa.



Ruwan kwakwa na maganin ciwon suga amma akwai bukatar nazari da bayani a yayin wannan hadin.


Ruwan kwa-kwa na kare koda daga barazanar ciwon nan na kidney stone.


Ruwan kwa-kwa na rage hauhawan jini.


Suna gyara lafiyar ciki su warkar da wasu cutuka kamar na kumburin ciki da tashin zuciya ko yawan gyatsa,


Karfin fahimta da aikin kwakwalwa sai a nemi dabino da zuma da ruwan kwakwa.

Wannan wani hadine na daban da za a ci moriyarsa. Domin Karin bayani.




Madarar Kwakaka (Coconut Milk)

Wannan madarace amma kuma ba irin wacce muka sani ba. Madarace da sai an niqa kwakwar sannan ake samunta.

Wannan ne yasa madarar Peak har yanzu ita ce akan gaba sabili da ana hada madarar ne da kwakwa.



Rabin cup daya na Madarar kwakwa na kumshe da calories 138.

Gram daya da rabi na protein

gram 2 na sugar

 Da kuma grams 14 na fat. Sai 5.5 milligrams  na manganese, milligrams 15 na copper,60 na phosphurus,  

22 na magnesium, sai 3.9 na Iron da kuma 4.5 na potassium

kashi hamsin na maikon dake a cikin madarar kwakwa lauric acid ne wadanda ke magance kwayar cuta ta bacteria da virus.




Madarar kwakwa na gina jiki ta bada karfi wa jiki ta kuma zamo sojojin da zasu kare jiki daga farmakin wasu cutuka.


Tana taimakawa masu anemia ganin tana dauke da sinadiran Iron a cikinta saidai basu da yawa amma duk da haka idan aka  sha za a fa'idantu.



Wanda ke son samarwa jikinsa da sha'awa sai ya nemi kilelen dabino ya hada da kwakwa ya tauna. ko a sanya madarar kwakwa a dama garin dabino dasu sai a dora akan wuta amma kada a tafasa da yawa dan idan zafin wuta yaiyi yawa to zai kashe wasu muhimman sinadirran dake a ciki.


Mai fama da ciwon ga6o6in jiki zai iya amfani da madarar kwakwa tana magani sosai.


Na so in yi ta kawo fa'idodin amma zan takaita anan.Tare da fatan za a amfana

Comments