Siffofin da za a gane Mace Mai Aji da kamun Kai.
__Itace macen da tasan darajar kanta da kuma addinita ta hanyar gujema duk abinda zai taba mutum cinta.
__Itace macen da bata shiga abinda babu ruwanta domin gudun kar arainata.
__ Itace a koda yaushe take suturta jikinta domin tana matukar kishin kanta.
__Itace wadda bata tara samari ko kuma kawaye barkatai saboda gujema kananan maganganu ko kuma a wulakanta ta.
__Itace macen da bata daukan raini don ba ta raina kowa itama bataso a rainata.
__Itace waddda bakajin hayaniyar ta a inda ake yawaita surutu don tafi kowa kishin muryanta .
__itace wadda bata saka hotunanta a social media saboda tana matukar tsoron abinda zaisa aga surarta
___Itace mace mai girmama duk wadda ya girmamata don tasan darajar su koda akwae wa'inda basa sonta.
__Itace komin sanda takema namiji bata bari har yaga fuskar da zaiyi wasa da sasan jikinta.
__Mace mai aji kana iya samun soyayyarta ammah ba cikin sauki bane zata iya bari ka shawo kanta.
__Mace mai aji takan koma mara aji a lokacin da take matukar sonka hakan nafaruwane saboda tunaninta kaine zaka aureta.
__Itace mace mai qualityn da kowani namiji yake mafarkin ganin ya aureta.
__Banbancin ne tsakanin jan aji da kuma girman kai da mace keyi ammah saika sa hankali gami da tsaida tunnaninka waje daya sanan ka nazarta.
___Yar uwa ki kasance mace mai aji koda kuwa mutane xasuyi ta sukarki da bakaken maganganu akanki hakan shawarace kyauta.
Comments
Post a Comment