Faidar cin dabino ga mace mai ciki,da kuma wadda ta haihu
Kamar yadda Abdul laɗif Ashur ya ambata acikin littafin Attadawi Bilaashab
Daga cikin ámfanin cin dabino ga mace mai ciki yace: "Haƙiƙa bincike ya tabbatar da tasirin cin ɗanyan dabino ga mace mai ciki.
Wanda yake ta'asirin Wannan dai dai yake da tasiri na allurai da ake yi ma mata masu ciki domin saukake haihuwa, da kuma kare lafiyar su data 'ya'yan da zasu haifa.
Kamar yadda yake taimakawa wajen kewayawar harmunat waɗanda likitoci suka bayyana.
Bayan haka yana taimakawa wajen rife mahaifa, bayan haihuwa, da kuma dawo da ita gurbin ta, da hana zubar jini mara Misali.
Bayan haka masana sukace cin dabino ga mace mai ciki yana bada kariya da ga haɗarin kamuwa da hawan jinin masu ciki, da dama a lokacin haihuwar.
Kamar yadda yake da ta'asiri wajen bada nishaɗi a gaɓɓan jiki, domin ta'asiri da yake yi akan algada darƙiyyah. wanda ake kira da yaran Ingilishi (Thyroid gland).
Idan muka koma acikn Alqur'ani mai girma acikin suratul Maryamu Alaihissalam inda Allah subhanahu wata'ala yake ce mata "وهزي
أليك بجذع النخلة تساقط أليك رطبا جنيا"
Allah madaukakin sarki yace mata taje wajen Wannan tushen dabino tagirgiza shi dabino danye zai fado mata.
Bayan haka Allah subhanahu yace mata taci tasha" فكلي واشربي وقري عينا"
Don haka dabino yanada amfani ga mata masu ciki alokacin dasuke ɗauke dashi har zuwa lokacin haihuwar da kuma bayan haifuwar.
Tun watan farko kuma yana gyara halitta ɗa tun aciki, ma'ana yaro yazama an haife shi kyakkyawa, koda kuwa iyayan sa munana ne.
Sannan cin sa bayan haifuwar yana taimakawa wajen dawo da Mahaifa gurbin ta da wuri, da bada karfin jiki ga mace wadda ta haihu.
Wallahu taala aalam.
Comments
Post a Comment