Hanyoyi biyu da za ayi tsarin Iyali (Planning) ba tare da Shan Wani magani ba balle matsala ta biyo baya.
Wadansu matan suna samun kansu cikin haihuwa akai akai (kwanika) wanda wata bata wuce shekara daya take sake haihuwa ko kasa da haka kuma hakan yana wahalar da ita dama yaran da take haifa basa samun ishashen kulawa to irin wadannan matan shari'a bata hanasu su rinka kayyade lokacin haihuwa ba
To saidai wani lokacin mata suna samun kansu acikin matsala idan suna shan maganin bature wajen dakatar da haihuwa har ma wadansu yana zama musu musabbabin dena haihuwa na har abada wasu kuma yana cutar da lafiyarsu
Shima dai maganin gargajiya yana iya kawowa mace matsala musamman wasan al ada ko kuma ciwon ciki sannan kuma zaki iya shansa be dakatar da Haihuwar ba wannan shine dalilin da yasa mutane da dama tambayar to wacce dabara za ayi domin abun ya zama cikin kwanciyar hankali ba tare da fargababa? abin nufi ya za ayi mace ta dakatar da haihuwa kuma ba tare da mijinta yayi amfani da kororon robaba? (condom)
To hanya ta farko dai itace (azalu) kuma tana da dogon tarihi domin tun zamanin sahabbai sunyi amfani da ita kuma manzan Allah (saw) be hana suba kamar yanda Bukari ya rawaito daga Hadisin Jabir dan Abdullahi mai lamba ta :4911.
Shi kuma yanda akeyin sa shine lokacin da namiji yake jima i da matarsa idan zai kawo maniyi sai ya fitar da gabansa yayi releasing a waje maniyinsa baya shiga farjin matarsa to babu damar yin ciki a haka.
Hanya ta biyu kuma lokacin da mace ta kammala al'ada to kwanaki uku zuwa 5 ko kwana 10 bincike ya nuna lokacinne mace ke daukar ciki to sai a daina saduwa a wannan lokacin domin kwayoyin cikin mahaifarta idan suka rasa maniyin namiji a wadannan kwanakin suna mutuwa to hakan shima zai hana mace ta dauki ciki..
Comments
Post a Comment