Hanyoyin da za abi wajen magance kyesbi da man kade
Sau da yawa masu fama da kyesbi sukan ce kyesbin ba ya jin magani, har sukan yi masa kirari da ‘kyesbi tsoho mai ran karfe, Idan wannan ce matsalar sai mu ce ku sha kuruminku domin mun taho miki da hanyoyin da za ki bi wajen magance kyesbi.
1. A karon farko, ki samu man kade wanda ba a sanya masa wani abu ba. Misali, man kade da ba sanya turare ko aka hada shi da wani mai ba.
2. Kafin ki yi amfani da man kade wajen magance kyesbi, yana da kyau ki shafa man a wani bangare na jikinki, misali, a kumatunki ko gefen kunnenki, kasancewar man kade na haifar da matsala ga wata fata. Idan bayan kin shafa man bai kuma haifar miki da matsala ba, sai ki yi amfani da shi wajen magance kyesbi.
3. Ki samu ruwa mai dumi, sai ki debi man kade, sannan ki zuba kofin shan shayi daya na gishiri a cikin ruwan da za ki yi wanka. Bayan kin yi wanka sai ki tsane jikinki da tawul mai kyau da kuma tsabta.
4. Daga nan sai ki shafa man kade a jikinki da kuma wurin da kyesbi ya fito miki, sannan ki rika yin tausa (massage) a wajen. Za ki iya yin hakan sau biyu a rana.
5. Bayan kin shafa man kade, sai ki guji sanya tufafi mai kauri, ko kuma mai kaushi wanda zai rika sosa fatar jikinki.
Wadansu hanyoyin magance kyesbi:
1==> Daga farko ki wanke duk wurin da akwai kyesbi da ruwa mai dumi, daga nan sai ki goge wurin da tsumma mai tsabta. Bayan nan sai ki samu man E45, sai ki shafa a wurin. Yin hakan zai magance kyesbi.
2==> Amfani da man da ke dauke da sinadarin ‘hydrocortisone’ na magance kyesbi. Daga farko ki yi wanka da ruwa mai dumi. Bayan nan sai ki shafa man. Ire-iren wadannan man suna busar da kyesbi. Amma kafin a yi amfani da ire-iren wadannan man kamata ya yi a nemi shawarar likitoci.
Comments
Post a Comment