Main menu

Pages

ILLOLIN YAWAITA CIN NAMIJIN GORO GA LAFIYAR JIKI

 



Illoli guda biyar da cin Namijin goro ke haifarwa ga Lafiyar Jiki.

 Namijin goro (Garcinia kola; a kimiyyance) dan itaciya ne da ke da tasiri wajen warkar da cututtuka da dama. Sai dai duk da wannan amfani da namijin goro ke yi, yana da illoli da kan iya yiwa jiki lahani. Ga wasu daga cikin illolin da namijin goro kan iya haifarwa ga jikin mutum da kuma lafia





 1. Namijin goro kan iya haddasa kansar baki (mouth cancer): Yawan cin namijin goro kan iya jawo ciwon dajin baki ko kuma uwar hanji. Namijin goro na dauke da sinadarin gahawa (caffeine) mai yawa, yawan gahawa a jiki kan iya kashe mutum ko ya jawo ma sa ciwon zuciya.





2. Namijin goro yana taba ido/gani (glaucoma): Cin namijin gora kadan na taimakawa ido/gani, sai dai cinsa da yawa na iya haddasa matsalar idanu. Akwai bukatar ya kula da adadin namijin goro da ya ke ci a rana.





3. Yana tunzura gudawa: Namijin goro na iya tunzura gudawa idan aka ci shi da yawa. Masana sun shawarci ma su fama da gudawa su guji cin namijin goro.





4. Yana tsinka jini: Masana sun bayar da shawarar cewar ma su rauni su guji cin namijin goro saboda yana jinkirta daskarewar jini. Kazalika an shawarci wadanda aka yiwa tiyata su guji cin namijin goro.





 5. Yana kara rikicewar kwakwalwa: Akwai wasu sinadarai a cikin namijin goro da ke kara tunzura matsalar rikicewar kwakwalwa, hakan ne ya saka masana bawa ma su matsalar rikicewar kwakwalwa kauracewa cin namijin goro.

Comments