Kalalolin Abinci Guda biyar da ke haifar da ciwon Hanta
Hanta dai wata tsokace mai matukar anfani, ta na taimakawa dan adam wajen lalata wasu kwayoyin jini da suka lalace.
Ana samun hanta ne a cikin dan adam Hanta dai wata aba ce mai matukar anfani a cikin jikin dan adam.
Ko shakka babu hanta mai lafiya kusan dai-dai take da mutum mai lafiya haka zalika hanta marar lafiya ma dai-dai take da mutum marar lafiya. Ga abubuwan dake mawo ciwon Hantar.
1- Abinci mai kitse.
Dukkan dange-dangen abinciccika masu kitse na da matukar hadari da lafiyar hantar dan adam. Abincin da ke da kitse yakan ba hanta wahala sosai kasantuwar ita ce ke kula sarrafa dukkan abunda ke shiga cikin dan adam. Yawan cin kitse kan cutar da ita sosai.
2- Sugar
Kadan daga cikin ayyukan hanta shine sarrafa suga zuwa sinadarin kitse kuma kamar yadda muka karanta a sama, yawan hakan ma kansa yana da lahali ga lafiyar hantar.
3- Gishiri.
Binchiken masana ya nuna cewa abinci mai gishiri kan yi lahali ga jiki musamman ma dai kasantuwar hanta ita ce ke da alhakin sarrafa sinadarin. Yawan gishiri kan wahalar da hanta ya sanya mata cuta.
4- Giya
Shan giya ma dai kan taimaka wajen lalata hantar dan adam kasantuwar cewa takan wahalar da hantar wajen sarrafa ta.
Allah Ya tsare mu Ya ba marasa Lafiya Lafiya.
Comments
Post a Comment