Main menu

Pages

KASAR JAMUS TA KIRKIRO WANI INJIN DIN KYANKYASAR JARIRAI

 



Iko sai Allah, Ƙasar Jamus Ta Kirkiro Injin din Kyankyasar Jarirai.


Kasar Jamus ta kirkiro wani inji da zai rika raino tare da kuma kyankyasar jarirai irinsa na farko a duniya.


Sunan injin ‘Ecto Life’ kuma zai samar da duk wani abu da jariri yake bukatar a cikin mahaifiyarsa har ma da kari.




An shafe sama da shekara 50 ana kirkirar wannan injin, wanda manyan likitoci da masana suka yi dafifi wajen tabbatuwarsa.


Injin zai iya kyankyasar jarirai 30,000 a cikin shekara guda.


A cewar wanda ya kirkiri injin a birnin Berlin na Kasar Jamus, Hashem Al-Ghaili, y ace injin zai kawo karshen matsaloli da mata ke fuskanta yayin daukar ciki, musamman masu fama da ciwon daji wanda likitoci suka ce ba za su sake haihuwa ba.


Kazalika, injin zai kawo mafita ga matan da ke mutuwa wajen haihuwa, matan da ake yi wa tiyata yayin haihuwa, matan da ke yawan barin juna biyu da sauransu.




Injin Ecto Life da zai ke kyankyasar jarirai

Injin zai taimaka wa kasashen da yawansu ke raguwa; Japan da Bulgeria da kuma Koriya Ta Kudu ta hanyar haifa musu yara masu yawa.


Ecto Life zai bayar da dama ga iyaye su koyawa jaririnsu irin yaren da suke so ya tashi da shi tun yana ciki.





Babban abin da ya fi daukar hankalin duniya game da ‘Ecto Life’ shi ne za a iya zabar wa jariri yanayin hallitar da ake so ya zo duniya da shi, misali za a zabar launin fata, yanayin ido, gashi da sauran yadda ake so sassan jikinsa su kasance.


Har wa yau, za a iya amfani da injin wajen kara kaifin basirar jariri.




A cewar Al-Ghalil, Ecto Life zai bai wa jarirai kariya daga kamuwa da cututtuka da suke kamuwa a lokacin da suke cikin iyayensu mata.


Sai dai abin tambaya a nan shi ne, duniya za ta karbi wannan injin ta rika amfani da shi, idan har hakan ta kasance, mece ce makomar iyaye ke nan wajen haihuwa?


A nan sai muce Allah Ya kyauta Ya cigaba da tsare mana imaninmu. 

Comments