Main menu

Pages

MUHIMMAN ABUBUWA GUDA BIYAR GAME DA TAFARNUWA

 



Muhimman abubuwa guda biyar game da tafarnuwa da ya kamata ku sani.

Tafarnuwa ta yi fice a yawancin dakunan girkinmu, ta kuma yi fice ta fannin lafiya.

Wata kwararriya a fannin abinci mai gina jiki, Kerry Torrens, ta yi nazari da bayani kan muhimmancin tafarnuwa.




Mece ce tafarnuwa?

Tafarnuwa daya ce daga cikin tsoffin tsirrai da ake shukawa, kuma daga cikin sinadaran da ake amfani da su dangin Liliaceae, wanda su ne tushen Albasa, da suransu.

Sun yi fice wajen ba da daddadan kamshi da dandano cikin abinci.

Dunkulen tafarnuwa kan kunshi sala 10 zuwa 20, ya danganta da girman ta.

Launin jikinta kafin a bare, ka iya kasancewa fari, ko launin makuba, amma da zarar an bare ta, komai fari ne a jikinta.



Curi guda na tafarnuwa na dauke da:

4Kcal/16KJ

0.3g gina jiki

0.0g maiko

0.7g mai sa kuzari

0.2g sinadarin narkar da abinci na fiber

25mg sinadarin potassium




Amfanin ta a likitance

Tafarnuwa na dauke da sinadaran da ke da amfani a likitance, sannan ana kiran yawancin abubuwan da ke cikin ta da allicin.


Sinadarin ne ke sanya kamshinta ya bambanta da na albasa, sannan dandanonta na daban ne.


Abin damuwa ga masu girki shi ne, matakin yanka ta, ko markadawa da ake yi yana rage sindarin allicin din da take dauke da shi.


An tabbatar cewa dora ta a wuta na rage mata amfani, don haka shawara ga masu sanya ta cikin abinci, su dinga zuba ta bayan abincin ya kusa dahuwa.




Rage hatsarin kamuwa da ciwon zuciya

Yawancin binciken da aka gudanar sun mayar da hankali kan amfanin tafarnuwa ga lafiyarmu, da amfaninta wajen rage hadarin ciwon zuciya da daidaita yawan kitse a jikin dan Adam.



Bincike da dama da aka gudanar kan amfanin tafarnuwa sun gano tana magance matsalar dunkulewar jini, hakan na nufin ana amfani da tafarnuwa wajen tsinka jini domin rage hatsarin bugun zuciya.



Haka kuma, tafarnuwa na magance ciwon hawan jini, saboda yadda take tace jini da yadda kuma zai dinga shiga sassan da suka dace a jikin mutum.




Rage hadarin cutar sankara

Sinadarin sulfur wato farar wuta wanda tafarnuwa ke dauke da shi, an yi nazari kan yiwuwar tasirin rage kaifin cutar kansa, har da kansa mai tsiro.



Yawancin abubuwan da aka gano suna da amfani a tafarnuwar sun hada da magance kansar mafitsara ta maza, da ciwon koda.



Binciken bai zurfafa ba, wannan ne dalilin da ya sa har yanzu ba a tabbatar da tafarnuwa a matsayin maganin cutar kansa ba.




An dade ana amfani da tafarnuwa wajen magance cutukan ƙwayar cuta ke haifarwa wato virus a turance.


Ana kiran maganin da aka yi amfani da tafarnuwa wajen hadawa da suna "Russian penicillin" saboda yakar cutuka dangin infection a turance.


Tafarnuwa na magance cutukan da suka shafi fata, kamar kuraje, da kyazbi da sauransu.


Akan matse maikon tafarnuwar a shafa kai-tsaye a jikin ciwon ko magungunan da aka yi amfani da tafarnuwa wajen hadawa.




Kara karfin kashi

Bincike kan dabbobi ya nuna amfani da tafarnuwa na kara kwarin kashi ga macen bera.


Wani nazarin kuma ya nuna tafarnuwa na taimaka wa mata lokacin da jinin al'darsu ya dauke, suna hadiyarta a kowacce rana.


Wani nazarin ya bayyana tafarnuwa na taimaka wa masu ciwon gwiwa, da rage radadin ciwon da magance sanyi wanda shi ne ciwon ba ya so.

Comments