Amfanin Ciyawar Shajarat Maryam ga Mace, da yadda Ake amfani da ita wajen Neman Haihuwa.
Shajarat Maryam wata ciyawa ce mai ganye da kuma fure da ake kira da suna daban daban kamar haka : "The flower of Maryam", "Anastatica hierochuntica", "Madina leaves", "Nabi booti", ko "Maryam booti".
Ana samunta a yankin gabas ta tsakiya, Palestine, Egypt, Jordan, Iran, Pakistan, Makka, Madina.
Larabawan dake a Makka da Madina da kuma masu maƙobtaka dasu sun ɗauki shekaru masu yawa suna amfani da Shajaratu Maryam a matsayin magani musamman dan sawaƙe wahala a lokacin da mata ke (Naƙuda) da kuma maganin rashin haihuwa a tsakanin matan da ke fuskantar rashin haihuwa ko ɗaukewar haihuwa sakamakon wasu matsaloli kamar na cysts, da Pcos (polycystic ovary syndrom) da makamantansu.
A duk lokacin da haihuwa tayi nauyi ma'ana (idan mace ta fara naƙuda to domin samun sauƙin wahalar naƙuda sai a nemi Shajarat Maryam kamar yanda kuke gani a hoto sai a nemi container a tafasa ruwa sai ya tafasa sai a tsomata a cikin ruwan sai a adanasu a cikin ɗakin mai yin naƙuda ta yanda hayaƙi da ɗumin ruwan zai kai gareta ko idan zata iya zatayi surace da ruwan.
A yayin da aka tsoma wannan ciyawar, to furen ciyawar ta Shajaratu Maryam zata cika kamar ana hura baloon baloon. wanda wata hikimace ta Allah da hakan zai sauwaƙe wahalar naƙuda, a cikin lokaci kuma cikin sauƙi zata haihu a cikin aminci da yardar Allah.
A wasu yankuna na Pakistan suna amfani da Shajarat Maryam dan maganin sanyin ƙirji waton (chest cold).
- Da rashin yin al'ada ko ɗaukewar al'ada ga mace na ba gaira ba dalili.
- Maganin farfaɗiya (epilepsy).
- Yawan zubar jini a yayin al'ada
- Ana amfani da ganyenta a turara gaba (farji) da shi ga mace mai fama da yankewar jini a yayin al'ada.
Su kuma matan dake neman haihuwa sukan yi amfani da garinta su haɗa ta da madara karamin cokali ɗaya su rinka sha da safe kafin a karya. za ayi hakan tsawon wata uku. sai dai kuma akwai wasu lokutan da ba za a shata ba.
Ana gauraya garin Shajaratu Maryam da man zaitun (Olive oil) da kuma zuma ƙaramin cokali sai a sha dan magance ciwon mara na mata da rikicewar al'ada.
- Ana dafa ganyenta da ganyen magarya a rinƙa amfani da ruwan ana tsarki dasu ga matan dake fama da ciwon sanyi (infection.)
- Ana amfani da ita dan maganin ciwon mara a yayin al'ada.
- Haka ko bayan an haihu to za aiya amfani da ita wajen yin suraci da ganyen. Tana da amfani sosai.
Tana da fa'idodi masu yawan gaske, Allah Ya datar damu dai dai.
Comments
Post a Comment