Jerin Sassake - Sassake da Saiwowin Itatuwa da yadda Ake sarrafa su wajen magance cututtuka.
Sassaƙe-Sassaƙe:
Sassaƙe na nufin yin amfani da fatanya ko magirbi ko dai wani abin wajen ciro ɓawo ko jikin wata bishiya domin a sarrafa ta a yi magani misalan kaɗan daga ciki sun haɗa da:
- Sassaken Kirya
Ana Amfani da sassaƙen ƙirya ana jiƙa shi da ruwa a sha yana maganin ciwon jiki.
- Sassaken Taura
Ana amfani da sassaƙen taura a jiƙa a sha yana maganin (Tamama) jin-kashi wanda yara ke fama da shi.
- Sassaken Marke
Ana jiƙa sassaƙen marke a ruwa a ba mata masu ciki wata huɗu idan yana yi musu ciwo domin samun lafiyar cikinsu da jaririn da suke ɗauke da shi.
- Bayana haka ana shanya sassaƙen marke ya bushe a daka a haɗa da irin gero idan za a shuka domin samun kyakkyawan sakamako, sannan kuma baya burtuntuna.
- Har ila yau ana haɗa sassaƙen marke da jar-kanwa a sha maganin tari.
- Ana sassaƙo bishiyar marke a dafa idan ya huce sai a ɗiba a haɗa da lemon tsami a rinƙa sha yana maganin tari.
- Sassaken Shirya
Ana jiƙa sassaƙen shirinya da ruwa a rinƙa ba yara suna sha maganin mafarkin yara. Kinkiba.
-Sassaken Tumfafiya
Ana kankare sassaƙen tumfafiya a haɗa da nono a sha maganin shawara.
- Sassaken Bakin Makarho
Ana sassaƙar baƙin-maƙarho a jiƙa da ruwa har tsawon kwana uku, a rinƙa sha maganin basir mai tsiro.
- Sassaƙen Farar Ɗorawa da Sassaƙen Mangwaro:
Ana amfani da sassaƙen farar ɗorawa da sassaƙen mangwaron a jiƙa da jar-kanwa a sha maganin basir.
- Sassaken Kwanarya
Ana dafawa da nonon saniya a riƙa sha yana maganin shawara, bayan an sha ana yin amai, ana warkewa sarai.
- Sassaken Gawo
Ana jiƙa sassaƙen gawo da ruwa a sha yana maganin taurin kai, musamman 'yan tauri ko 'yan daba.
- Sassaƙen Goba da Mangwaro da Lemon Tsami:
Ana amfani da su wajen maganin ciki, ana shanya su, su bushe sannan a daka a rinƙa jiƙawa ana sha yana maganin ciwon ciki.
- Sassaken Ararrabi
Ana jiƙa sassaƙen Ararraɓi a rinƙa sha yana maganin tau-tau, bayan haka ana shanyawa ya bushe a daka a rinƙa barbaɗawa a kan tau-tau ɗin.
SAIWOWI
Saiwoyi na nufin wasu jijiyoyi ne ƙananan da manya waɗanda su ke riƙe da bishiya ko tsirrai. A koda yaushe saiwoyi kan kasance ne a ƙarƙashin ƙasa amma a wani lokacin sukan fito waje ma'ana su kan turo ƙasa.
A ɓangaren magungunan Hausawa na gargajiya su ma ba a barsu a baya ba, domin kuwa suna bayar da gudunmawa ta musamman wajen warkar ko kwantar da cuta a jikin Ɗan-Adam ko dabba. Wasu daga cikin saiwoyin da ake haɗa magungunan Hausawa na gargajiya sun haɗa:
- Saiwar Kuka
Ana haƙo saiwar kuka wadda ta ratsa kan hanya, ana haɗa maganin kwarce da kuma maganin soyayya. Akan haɗa abinci da ita a ba yarinya ta ci, maganin mallakar zuciyarta domin soyayya.
- Saiwar Tafashiya
Mata masu ciki na amfani da saiwar tafashiya, su jiƙa su sha domin samun lafiya cikinsu.
.
- Saiwar Gaude
Ana haƙo saiwar Gauɗe a jiƙa a rinƙa sha, yana maganin ƙarfin jiki.
- Saiwar Rawaya
Ana jiƙa saiwar rawaya a sha, ko kuma a shanya ta bushe a daka a rinƙa soyawa da ƙwai ana ci yana maganin shawara.
- Saiwar Bakin Gagai
Ana jiƙa saiwar baƙin gagai da kayana ƙanshi a riƙa sha maganin ƙarfin maza.
- Saiwar Sabara
Ana ɗebo ko haƙo saiwar sabara da saiwar lemon tsami da ganyen tsamiya a haɗa a daka, sannan a jiƙa rinƙa sha, yana magann tamama (shawara) kamar yankan wuƙa.
-Saiwar Jema
Ana haƙon saiwar jema a wanke a zuba a randa ko ruwan sha, tana maganin mayu.
- Saiwar Dayi
Ana haɗa saiwar dayi da farin goro a tauna sannan a haɗiye ruwan, tana maganin farin jinni. Bugu da ƙari idan aka tauna saiwar dayi ita kaɗai aka haɗiye ruwan maganin sammu (Makaru).
- Saiwar Tafasa
Ana haƙo saiwar tafasa a dafa da jar kanwa tana maganin ciwon nono
- Saiwar Zogale
Ana haƙo saiwar zogala a haɗa da saiwar bini da zugu da lemon tsami da kuma barkono a jiƙa a sha, yana maganin sanyi mai kumbura jiki.
Comments
Post a Comment