Yanda Ake hadadden Tsumin Kankana don wanzuwar tabbatacciyar Ni'ima ga Mace.
Tabbas mace komai kyawunta idan bata da ni'imar jiki to bata iya gamsar da mijinta, dole ayi mata kishiya, to amman ni'imar mace ya dan ganta da irin nau'in abincin datake ci.
Amman matsalar itace basa tuntubar masana dan basu haske sai dai kawai suyi ta sayan magungunan 'yan kasuwa wanda basa dadewa jikinsu wasuma basa aiki.
Ga duk macen dakesan samun ni'ima a jikinta tota liqewa wannan sinadarin.
Kuma ana hadin ne da dare idan sun jiku da safe ake sha.
1. Asamu kankana (water milon) meyashi se a fafe samanta da wuka ayi mata kofa.
2. Asamu kanumfari (Clove) a dakashi a zuba acikin kankanar.
3. Asamu dabino a nikashi a zuba a cikin kankanar.
4. Kwakwa (coconut) kwallo daya a fasa ta a zuba ruwan cikin kankanar sannan kwakwar ma a nika ta a zuba cikin kankanar.
Sai a rufe kankana saida safe sun jiku sai uwargida ta shanye ruwan tas sannan ta cinyen kankanar.
Zaki bawa kawarki labari.
Anaso mace ta yawaita wannan abun zatai kima da martaba ga mai gidanta.
Kila ma maigida ya baki kyautar jirgi saida safe ayita rigima.
Insha Allahu duk wacce tayi amfani da wannan sinadarin zata yaba kuma zata kara yiwa Allah godiya.
Comments
Post a Comment