Main menu

Pages

YADDA SANYA WUTAR DAKI KO RUSHI KE ILLATA MUTANE

 



Yadda Sanya Wuta Ko Rushi a daki ke Illa tare da kashe rayuka a lokacin sanyi.


A wannan lokaci da sanyi ke ƙara kankama, a kiyaye da shiga ɗaki da gaushi ko wuta mai ci tare da rufe ƙofofi da tagogi.



Zaɓi sanya gaushi ko wuta a ɗaki kafin lokacin kwanciya idan ana son ɗumama ɗaki. Idan ɗakin ya yi ɗumi sai a fitar da gaushin ko wutar waje. 



Kada a ruɗu da cewa wutar ko gaushin ba ya hayaƙi, domin matuƙar gaushin yana ci to yana fitar da wannan gurɓatacciyar iska.



Ajiye gaushi a ɗaki tare da rurrufe ƙofofi da tagogin da iska za ta zagaya na da illar gaske. Shaƙar iska daga makamashin da ke cin wuta na fitar da hayaƙi ko iska mai gubar da shaƙarta na da lahanin gaske ga hanyoyin numfashi, huhu, jirkita lafiyayyiyar iskar oksijin cikin jini da kuma lahani ga ƙwaƙwalwa, laka da jijiyoyin laka. Wannan matsala na lashe rayukan mutane da yawa musamman ƙananan yara lokacin sanyi duk shekara.




Ƙananan yara suna daga cikin waɗanda suka fi samun wannan matsalar sakamako ba za su iya magana ba yayin da gurɓatacciyar iskar ta ci ƙarfin su. 

Allah Ya tsaremu da faruwan hakan.

Comments