Main menu

Pages

YADDA YA KAMATA KIYI AMFANI DA KURKUM WAJEN GYARA FATARKI

 



Yadda za ayi amfani da kurkum don samun ingantacciyar Fata.

Kurkum na dauke da sinadarai da dama kamar su, bitamin B6 da bitamin C da sauransu. Kuma yana rike fata yadda ba za a sami rauni ba. Yawan amfani da hadin kurkur na sanya fata musamman ta fuska laushi da santsi da kuma haske. Don haka, ya kamata kada a manta da wannan kurkur idan an zo kwalliya.  Amfani da kurkum na sanya sabuwar fata fitowa da wuri a inda tsohuwar ta fita ko ta sami matsala.





•A sami garin kurkur da zuma cokali daya da ruwan lemon tsami kwatan kofi. A kwaba su sosai har sai sun yi laushi. Sannan a shafa a fatar fuska a bari ya jima na mintuna 15 sannan a wanke da ruwan dumi. Yin wannan hadin na hana kurajen fuska fesowa. Za a iya yin wannan hadin kamar sau daya ko biyu a sati domin samin ingantaccen sakamako.





•Amfani da kurkum na rage gautsin fuska. A kwaba kurkum da nono ko kindirmo. Sannan a wanke fuska kafin a shafa hadin a fuska. A jira na tsawon mintuna 10-15 kafin a wanke. Za a iya jarraba wannan hadin a kullum bayan an yi wanka.





•Idan ke mai yawan aiki a karkashin rana ce, ya kamata ki samu kurkur kadan da kindirmo mai yawa sai ki rika shafa wa a inda kunan rana ta bata fuska. kunan rana na sanya fuska ta zama kamar mai shafe-shafe don haka wannan hadin zai magance wadannan matsalolin.





•Ko kun san cewa kurkur na magance bakar fatar karkashin hammata? To! A sami zuma kamar cokali daya sai a hada da ruwan lemon tsami kamar cokula 3-4 sai a zuba garin kurkum kadan sannan a kwaba a shafa a karkashin hammata a bari ya jima na tsakwon mintuna 10-15 kamin a wanke. Allah ya bamu dacewa Ameen

Comments