Yanda Bishiyar Kalgo ke maganin kusan dukkan Matsalolin Mata, har da wasu Mazan cikin yaddar Allah
Bishiyar kalgo wata bishiyace wadda Allah (S.W.A) ya albarkaceta da sunadarai masu karfin gaske wajen magance wasu matsaloli dakuma yakar cututtuka daban daban daka iya tasiri a jikn Dan Adam.
Wannan bishiya anfi samuntane a kasashen africa da Asia inda shekaru da dama da suka wuce ana sarrafa wannan bishiya domin nau'ikan magunguna kala kala.
Yadda Ake sarrafa wannan Bishiya
(1) Ana zuba garin sassaken kalgo da sassaken baure cikin abinci ko atafasasu da madara kokuma haka nan ajika garin da ruwa asha ko cikin shayi domin maganin ciwon sanyi ( gonorrhea ) da sauran cututtuka da ake iya dauka wajen saduwa.
(2) Ana dafawa ko ajika saiwar ko ganyen ana shan ruwan domin maganin rikicewar Al'adah, yawan bari, ko kuma daukewar jinin Al'adah.
(3) Ana dafa saiwar kalgo ana shan ruwan domin yana maganin ciwon mara lokacin Al'adah.
(4) Ana dafa saiwar kalgo aba Macen da ta haihu domin inganta lafiyarta.
(5) Ana dafa ganyen kalgo ayi wanka da ruwan domin saukaka ciwon jiki.
(6) Tauna ganyen kalgo bayan andafa shi yana maganin ciwon hakora.
(7) Ana dafa ganyen kalgo ashafa inda kai yake ciwo insha Allah zai daina.
(8) Ana tafasa ganyen kalgo ayi wanka dashi yana maganin masassara.
(9) Ana shafa tokar kalgo a kirji domin maganin ciwon kirjin.
(10) Ana amfani da garin sassaken kalgo domin maganin ciwon makoshi, ciwon hakori, ciwon kunne, ciwon ciki da kuma maganin kasala da ciwon jiki.
(11) Ana zuba garin sassaken kalgo ga rauni domin yayi saurin warkewa.
Wannan kadanne daga cikin amfanin kalgo. Allah Ya sa a dace
Comments
Post a Comment