Hanyoyin Karfafa Hasken Kwakwalwa da Karin Fahimta da magungunan Musulunci da abinci.
Zamu kawo wasu hanyoyi daban daban, Kamar yadda muka fada a sama akwai magunguna da Kuma abinci dake kaifafa Kwakwalwa.
Daga cikin abinda ake yin magani dashi, kuma abincine mai Kara lafiyar jiki ta kowacce wanda yake Kara karfin kwakwalwa, da kuma kara basira akwai.
- Yawan cin Zabib.
- Ziitir.
- Man zaitun.
- Lauz, namijin goro.
- Ayaba.
- Dabino.
- Bakar Zuma.
- Tafarnuwa.
1. Zanjabeel (Danyar Citta) Hada Ziitir da man zaitun idan ana amfani dashi yana farfado da kwakwalwa, da kuma taimakawa wajen tuno ma kwakwalwa abinda ta manta.
2- Anacin tafarnuwa kwara daya bayannan Sai aci dabino kwara (7)
3- Za a iya samun Lubbana zakar, da kuma sukari nabat, da Zanjabeel za ayi garinsu ahada waje daya sai arika shan karamin cokali aruwan shayi sau uku arana.
4- Domin bama kwakwalwa nisahdi za a samo Alkamah adafa za a iya hadawa da bakar Zuma aci ita ma tana bama kwakwalwa nisahdi, da Kara karfin kwa kwalwa.
5- Ana samun hims arika dafawa anaci domin karama kwakwalwa nisahdi.
6- Idan anacin dabino yana kara ma jijiyoyin da suke kewaye da kwakwalwa karfi, da kuma aikin su yadda yakamata.
7- Kasamo Zanjabeel 100g
- Habbatusauda 50g
- Hindibau 50g
Za ayi garinsu a samo Zuma Mara hadi akalla kilo daya sai adinga shan babban cokali bayan kowanne cin abinci, Karamin yaro za a bashi Karamin cokali bayan kowanne cin abinci.
8- Ko kuma asamo garin habbatusauda yadda kake bukata, tare da Lubbana zakar, da kuma asalin Ziitir, da Zanjabeel, wadannan itatuwa ana bukatar yawansu yazama dai dai wadaida Sai ahada su waje guda sai ahada da Zuma Mara hadi kilo guda za a rika shan cokali dai dai sau uku arana.
9- Ko kasamo ganyan Naa Naa Karika yin shayin sa kasanya Zuma Mara hadi, bayanan kadiga man habbatusauda na asali sai kasha, ko karika bama yaranka suna sha.
10- Ko arika tafasa ganyan Na'a Na'a ana diga man habbatusauda ana sha.
11- Ko kasamo Zuma Mara hadi karika sha safe da rana da yamma.
Allah Ya Kara mana kaifin kwakwalwa da Fahimta.
Comments
Post a Comment