Hanyoyin da za a bi don Kaucewan kurajen fuska da yadda za a magancesu idan sun fito
Fitowar kuraje a fuska na daya daga cikin ababen da ke bata kwalliyar mace. Wasu kurajen duk hodar da aka sanya musu, ba ta iya boyar da su a lokacin kwalliya saboda tsabagen girmansu. Shi ya sa na kawo muku yadda za a bi domin kare fuskarmu daga fitowar kuraje ta hanya mai sauki.
Kamar yadda ake cewa rigakafi ya fi magani. A samu zuma mai kyau sai a hada ta da ruwa sai a sha kullum da safe domin samun fatar fuska mai santsi.
Ko kun san cewa turara fuska da ruwan dumi na kore miyagun kuraje daga fitowa?
Turara fuska na bude ramukan gumi wadanda suka toshe domin gumi da kuma dauda. Idan gumi da dauda suka toshe ramukan fitar gumi a fatarmu, sai ya zama maiko wanda zai haifar da fitar kurajen fuska. Turara fuska na taimaka wa jinin jikinmu wucewa ba tare da bata lokaci ba.
Domin hanyoyin su zama a tsabtace don gyara fuskar. Za a iya turara fuska a gida. Yadda ake turara fuska A tafasa ruwa a tukunya sai a hada ta da ganyen ‘thyme’ da ruwan lemun tsami. Bayan ruwan ya tafasa, sai a sauke shi daga wuta.
Sai a rufe kai da tawul domin turirin ruwan ya turara fuskar amma a dan yi baya da robar ruwan zafin kadan domin kada a kone. Turara fuska sau daya a mako na kare fuska daga fitowar miyagun kuraje. .
Kurajen fuska ko pimples a turance wasu kuraje ne da suka fi fitowa a fuska musamman idan mutum yana ta’ammali da mayuka iri-iri ba tare da kula da man daya dace da fatar fuskar ba.
Matsalar kurajen fuska tafi shafar Mata musamman matasa inda za’a ga wasu matan har nikab suke sanyawa a fuskokin Su saboda kar aga ta’adin da kurajen suka Yi musu a fuska.
Maza ma sukan fuskanci irin wannan matsala ta kuraje a fuska sosai.
Kadan daga cikin Abubuwan dake janyo kurajen fuska sun hada da:-
(1) yawan cin Abu Mai maiko.
(2) Amfani da mayukan da Basu dace da fatar fuska ba
(3) Kwayoyin cuta
(4) Shiga rana sosai
Mutane da dama kan kashe makudan kudade don sayan maganin da zai magance musu kurajen amma kuma yawanci ba’a samun biyan bukata. Ana iya magance kurahen fuska ta wadannan hanyoyin :
(1) Bawon lemon zaki:
Ana shafa bawon lemon zaki a inda abin ya shafa Sai a barshi ya kwana da safe Sai a wanke da ruwan dumi.
(2) Zuma:
Ana samun zuma Mai kyau a goga da auduga a fuska, a barshi zuwa Yan mintuna Sai a wanke. Za’a iya maimaitawa kamar sau biyu a rana har kurajen Su fita.
(3) Ruwan lemon tsami:-
Ruwan lemon tsami wata sahihiyar hanya ce mai matukar amfani wajen maganin kurajen fuska. Lemon tsami yana taka rawar gani sosai wajen kashe kananan kwayoyin cuta a fuska da kuma fitar da maikon fuska. Yadda za’ayi amfani da lemon tsami shi ne a samu lemon tsami a matse ruwansa sai a samu auduga mai tsafta a dinga goge fuska dashi kafin a kwanta bacci, da safe sai a wanke fuskar da ruwan dumin. Za’a iya maimaitawa sau biyu ko uku a rana har kurajen su fita.
(4) Ganyen darbejiya / Man darbejiya
Ana kwaba ganyen darbejiya da man darbejiya a shafa a fuska zuwa mintuna biyar sai a wanke da ruwan dumi ko a dinga shafa man darbejiya da auduga a fuskar har zuwa lokacin da kurajen zasu baje. Kurajen fuska dai sun dade suna batawa mutane fuskokin su har ta kai wasu ma sun gaji da nemawa kansu magani, mata ma kan yi duk yadda zasuyi su rufe fuskokin su don kar a ga kurajen,wasu ma kanyi amfani da hodar foundation akai akai don boye kurajen dake fuskar su. Wannan hanyoyi da na lissafa da karin wasu zasu taimaka sosai wajen cire kurajen fuska cikin sauki ba sai mutum ya kashe makudan kudade ba wajen neman magani ba.
Comments
Post a Comment