Yadda Zaki gyara jiki da Hadin Ayaba da Fiya, don samun kyawun Fata da taushi.
Fiya da ayaba na matukar taimakawa wajen gyara fatar jiki, sukan sanya fata ta yi sheki da kuma laushi. Kayan hadi:
· Ayaba
· Fiya
· Yogot
· Man zaitun
Yadda za a hada:
1==> Daga farko ki samu ayaba, sai ki bare, ki yasar da bawon, daga nan sai ki samu fiya, ki bare ta, sai ki zubar da bawon. Bayan nan sai ki hada ayaba da fiya da kuma kwallon fiyar, sannan ki daka.
2==> Bayan kin gama dakawa, sai ki zuba yogot da kuma man zaitun. Za ki ci gaba da cakudawa har sai kin tabbata komai ya gaurayu.
3==> Daga nan sai ki shafa a fuskarki ko jikinki har na tsawon minti 15.
4==> Bayan nan, sai ki wanke fuskarki ko sauran jikinki da ruwa mai dumi.
Comments
Post a Comment