Jerin cututtuka biyar da gemun Masara ke magancewa cikin yaddar Allah
Ga jerin cututtuka da ake amfani da gemun Masara wajen samun waraka daga Allah Insha Allah.
(1) Ciwon suga(diabetes)
(2) Matsalar fitsari(urinary infection)
(3) Fitar da dutsen qoda(kidney stone)
(4) Ciwon hawan jini(hypertension)
(5) Ciwon sanyi mai riqe gabobi(arthritis)
(1) Yadda ake magance diabetes za a sami gemun masara cikin Kofi sai asami ganyen yadiya cikin Kofi sai ganyen mangwaro cikin Kofi sai akirbasu, bayan ankirbasu sai azuba atukunya adafa idan ya dafu sai a sauke, asha Kofi daya da safe daya da yamma kuma duk lokacin daza asha sai an dimamashi, ayi haka har zuwa sati uku sai aje ayi gwaji agani, kuma yana da kyau akiyaye abinci da za a riqaci kamar yadda likitoci suka qayyade.
(2) Yadda ake Amafani da’ita game da matsalar fitsari za a samu gemun masara cikin kofi sai asami lemun garas shima haka sai adafa ‘ ariqasha kaman shayi.
(3) Yadda ake magance dutsen qoda(kidney stones)asami gemun masara cikin Kofi sai yayan zogala rabin Kofi sai ganyen zogala shima rabin Kofi sai akirabasu ko ayi blending azuba ruwa kofi daya da rabi aciki sai atace ashanye ayi haka sati uku
(4) Yadda ake magance hawan jini asami gemun masara Kofi uku sai jan zobo kofi daya sai yayan zogala rabin Kofi adafasu atace azuba awani abu a riqa sha safe da yamma Har sati daya ” bayan angama ana iya sakewa.
(5) Asami gemun masara kofi uku da tafarnuwa rabin Kofi da kanunfari cokali Bihar abusar dasu ayi garinsu ariqasha acikin madaran shanu ,bana gwan-gwani ba.
Ataimaka ariqa sharing(turawa)saboda Amfanuwan Al-ummah.
Comments
Post a Comment