Kalolin Abincin guda goma dake karawa Mace kugu, wato Hips. Sai a jure cinsu.
Baya ga motsa jiki na musamman da mace da take son kugunta ya kara girma zata yi, da akwai kuma wasu abinci na musamman da mace zata rika ci idan tana son kwankwasonta ya bude.
1: Kifin Salmon; Cinsa yana samarwa mace karin duwawu saboda kifin na dauke da sinadarin proteins mai yawa da kuma sinadarin Omega-3.
Don haka idan mace na da burin kara girman mazaunanta, ta yawaita cin wannan kifin da ake kira Salmon a turance.
2: Yawan cin kwai ; Shima yana kara girman kugun mace a binciken da aka gudanar.
Yawan cin kwai ga mace yana samar mata da sinadarin leucine da amino acids da suke karawa kugun mace girma.
3: Yawan cin Brown Rice; shima yana kara girman mazaunai ga mata.
Shi wannan nau'in shinkafa yana dauke ne da sinadarin carbohydrates da kuma sinadarin proteins.
Hakan yasa yawan cinsa ga mace zai karamata girman jiki da kuma baya.
4: Avocado wato Fiya; shima yawan cinsa ga mace na sawa ya kara mata girman mazaunai.
Yawan cin wannan cima yana samar da sinadarin potassium a jikin mace yadda zai kara mata girman mazaunai.
5: Bayan duk motsa jiki idan mace zata samu kaza ta rika ci. Cikin karamin lokacin zata tara kaya a bayanta.
Yawan cin kaza a cewar masana na samar da sinadaren proteins, vitamin da kuma mineral. Wanda dukkaninsu sinadare ne da suke gyara jiki da kuma kara girma.
6: Shima waken soya yana da matukar amfani wajen karawa mace girman baya idan tana yawan amfani dashi.
Ganin yadda yake dauke da sindarai masu kara girman jiki da baya.
7: Shan madara musamman mara sugar a ciki shima yana sa mace bayanta ya kara girma.
Ana so duk bayan motsa jiki mace ta samu madara ta kwankwada idan tana son kara girman kugu.
8; Yawan cin ganye irinsu zogale, rama da sauransu. Suma masana harkar abinci sunce suna iya karawa mace girman baya.
9. Shan shayi me kauri kullum kafin kwanciya bacci
10. Hadin gyaran nono da kiba da ake hadawa suma suna Kara girman baya.
Wadannan sune wasu daga cikin abincin da mace zata himmantu wajen cinsu muddin dai tana burin samu kugu ba tare da amfani da magungunan bature ba.
Sai dai dole sai mace ta hada da wasu motsa jiki na musamman da kuma yiwa bayanta tausa da man kwakwa ko na ayu idan tana son cimma burinta cikin karamin lokaci.
Comments
Post a Comment