Main menu

Pages

ABUBUWA GUDA 18 DA ANGWAYE YA KAMATA SU SANI

 



Sako Zuwa Ga Sabbin Angwaye da ma wadanda suka dade a cikin Auren.


1. Ka sani aure ibadane a cikin dukkan  ibada da ruyawar akwai jarrabawa a cikin  sa, hakuri, kiyaye dokokin da Allah da koyi da sunnan Annabi zai kaika ga cin nasara a ciki. 



2. Ka sani Amanace a wajen ka kuma Allah zai tambayeka akan amanar da aka damqama. 



3. Iyayenta sun baka ita ne dan kyauta zato a gareka akan 'yar su zata samu kuluwa da farin ciki a wajen ka, sabida haka kazama gatanta, karka sake ka samarmata da aqasin haka domin zai nuna gazawarka da qasqanci a matsayin ka na jagora. 



4. Kiyaye dukkan hakkokinta da ya rataya akan ka. 



5. Ka sani ita mace da kyauta da kyautata mu'amala aka fi sace zuciyarta, ka kasance mai kyautatawa a cikin kalamanka wajen mata gyara da kiyaye furta abunda zai cutar da zuciyarta, ka kyautata a cikin ciyarwa, tufatarwa, mu'amalantarta da 'yan uwanta. 



6. Ka sani mace halittace mai taushi zuciya da raunin hankali, wani lokaci zakaga abunda kake so wani lokaci sai kayi hakuri matuqar hakuri da kawaici da ita. 



7. Ka sani kai jagora a gidanka dan haka dole ka kasance abun koyi a cikin dabi'u da halaye a cikin gidanka. Kar ka bari munanan dabi'un ka ya zama abun kyama da zargi a cikin gidan ka, matuqar baka kiyaye naka ba zaiyi matuqar wuya ta iya kiyaye nata, wadda yin hakan zai zama silar fititintunu a auren ku. 




8. Kiyaye tsabtar jikinka, babu wadda yake son kusantar kazamin mutum, ka kasance mai kiyaye tsabtar jikinka a duk lokacin da zaka kusanci matarka, wannan zai samar mata da nitsuwa a zuciyarta da zata mu'amalance ka cikin kwaniyar aurenku cikin sauqi. Bayan tsabta, askin sama da qasa da yin brush atleast safe da dare, Ka riqe turare dan shine zai zama dan saqonka zuwaga matarka cikin sauqi. 




9. Ka kiyaye shigan 'yan uwanka al'amuran rayuwar gidan ka ko tsakaninka da matarka, cikin sauqi in baka iya tsayarda kowa a matsayar sa ba za'a dagulama lissafi da rayuwar gidanka akan abunda bai kai ya kawo ba a hanaka zaman lafiya da jin dadi da iyalanka. 




10. A duk lokacin da kuka samu matsala ka bada kofar zama tattaunawa a tsakanin ku domin shine kofa mafi sauqin samu gyara, mafita da maslaha a tsakanin ma'aurata.




11. Matarkace, ka karanceta kasan waye ita da yadda take mu'amalantar mutane, Karka bari wani ko wasu su zo suna fadama waye matarka domin aqasarin lokaci qarya ko sharrinta za'a fadama ba alkhairintaba. 




12. Ka sani a cikin zamanku zakaga abunda baka so a game da ita, ka tuna itama haka zata gani akan ka, so kuyi hakuri akan wadannan ku na yawan tuna kyawawan halayen juna dan su zasu kasance abunda zasuna kawar muku da wadanchan munanan halayen. 




13. Ka kasance mai kawaici kuma mai gyara a cikin gidanka ba mai dagula lissafiba. 




14. Ka sani namiji mai wasa da raha da iyalansa yafi samun walwala da jin dadi a cikin aure fiye da miji mai tsare gida. 




15. Ka kasance mai iya bada hakuri in kayi ma matarka kuskure domin yafi sauqi kuma yakan karka lagwan fitintunu da dama a tsakanin ma'aurata.




16. Ka sani yadda kake da hakki akan matarka wajen kwanciyar aure haka take dashi akan ka, karka kasance marowaci ko mai kauracewa matarka ba tare da dalilin da musulunci ya tanadarba dan akwai cutarwa a ciki sosai, kuma kofar bude fitinane sosai a aure da rayuwa duka.  




17. Ka zaman to da ita abokiyar shawara ko da kuwa ba lallai kayi aiki dashi ba, yin hakan zai baka damar sanin irin hankali da tunaninta wadda zhakan zai baka damar mata gyara a cikin tunanin ta. 




18. Ka zamto mai iya amsan uzuri domin shi dan adam ajine mai kuskure ne, kai ma zaka iya kuskure kuma zaka so tama uzuri. Kuma yin uzuri ma juna yakan rufe kofofin fitintunu da dama a aure.

Comments