Amfanin Abarba guda Sha uku ga Lafiyar Dan Adam
Musamman ma kare jiki daga kamuwa da ciwon zuciya. Abarba na daya daga cikin yayan itatuwa masu amfani a jikin dan adam.
Abarba na da matukar amfani a jikin dan adam saboda tana dauke da muhimman abubuwa irinsu, fibres, menirals, vitamins, Nutrient da kuma Anti Oxidant.
Wadannan sinadarai dake a cikin abarbar na da matukar amfani ga rayuwar dan adam, sannan takan kare jiki daga cututtuka.
Ga kadan daga amfanin Abarba
1- Tana dauke da sinadarin magnees da calcium wanda ke kara karfin kashi
2.- Tana dauke da anti oxidant wanda ke kara ma jiki lafiya da kare jiki daga saurin tsufa.
3. -Tana maganin mura da sanyin kirji.
5. - Tana kara ma garkuwar jiki lafiya da kare shi daga cututtuka.
6.- Tana maganin kamuwa da ciwon zuciya ta hanyar rage cholesterol a jiki.
7.- Tana kara lafiyar dasashi da kare hakora.
8. -Tana saukaka yawan laulayin ciki, da yawan amai da yawan tashin zuciya.
10.- Tana maganin tsutsar ciki.
11.- Tana kara ma idanu lafiya
12.- Tana kara lafiyar ciki da saukaka bahaya
13. - Tana maganin kumburi da maganin ciwon ga babuwa da fatan zamu rinka shan abarba akai akai.
Comments
Post a Comment