Amfanin Dinya Guda biyar ga duk Wanda ya juri shanta lokaci Zuwa lokaci.
Kamar yadda muka saba daga lokaci zuwa lokaci mu kan zakulo maku hanyoyin da za ku kara samun lafiyar jikinku, musamman ma ta hanyar amfani da abubuwan da ke zagaye da mu. Yau ma kuma gamu dauke da alfanun ‘ya’yan itacen nan bakake na dinya.
Dinya dai da ake kira da ‘Black plump juice’ a turance itace ne da kan fito a gonakin mutane tana yin girma sosai, sannan kuma tana fitar da bakaken ‘ya’ya a tare da ita da ke kama da na kanya.
- Tana taimakawa wajen gyaran ciki da dukkan maganin matsalolin da ke tattare da hakan kamar gudawa.
- Tana maganin cututtukan da suka shafi hakora da ma baki gaba daya.
- Tana maganin dankanoma da basir mai tsiro.
- Tana maganin tari da kuma cutar Asma.
- Tana maganin mura da kuma karin karfin garkuwar jiki.
Dinya tana magance wadannan cututtuka ne idan aka sha ‘ya’yan itacen. Domin haka sai mu ci gaba da shan ‘ya’yan dinya domin samun ingantaccen lafiya.
Comments
Post a Comment