Main menu

Pages

DALILAN DA KESA MATSALAR TABIN HANKALIN KE TASHI CIKIN SANYI

 



Mecece alaƙar da ke tsakanin sanyi da lafiyar ƙwaƙalwa? Da dalilin yawan Tashin matsalar lokacin sanyi.


"Babu wata cikakkiyar alaƙa da za a ce ga ta musamman, kawai dai wasu abubuwa ne aka kula a wasu a cikin nau'ukan ƙwaƙwalwa suka fi tashi ba kowanne ba," in ji shi.



Ya ƙara da cewa abin da ya sa aka fi ganin haka shi ne yawancin waɗannan nau'ukan na ciwon ƙwaƙwalwa na da yawa a cikin al'umma to shi ya sa tun da suna da yawa a cikin al'umma sai aga kamar ƙaruwa ya yi, sai mutane su kula cewa ana samun ƙaruwar mutanen da ke samun wannan matsala.



Dakta Auwal Fatuhu Abubakar ya ce: "Idan baya zuwa asibiti, to ya kamata ya ziyarci likita, idan kuma aka ga alamun ciwon zai tashi sai a yi sauri a mayar da shi asibiti domin a mayar da shi kan magungunan da yake sha."



Alamun da za a iya gane ciwon mai taɓin hankali na neman tashi.

- Rashin samun bacci ko baccin zai ragu

- Karuwar kasala da rashin jin kwarin jikin mutum zai karu

- Damuwa da ɓacin rai za su ƙaru

- Yawan fushi na ƙaruwa

- Za a ga mutum yana janye kansa daga cikin jama'a sannu a hankali

- Zai riƙa tunani iri-iri, ciki har da na son kashe kai

- Zai riƙa jiye-jiye da gane-ganen abubuwan da ba kowa ne ke ganinsu ba.

- Wani taimako za a iya yiwa mutum kafin kai shi asibiti?



A cewar Dakta Auwal Fatuhu Abubakar idan aka kula canji ya soma faruwa ga halayyar mutum to idan yana da magunguna ya kamata ya fara amfani da su.


Sannan ya kamata ya kiyaye, ko ƴan uwansa su kiyaye masa ka'idojin da likita ya gindaya masa.



"Ya danganta da tsananin ciwon, wani za ka ga na dan lokaci kankani ne, wasu kuwa sai an dan kwana biyu ana shan magani sai ka ga ya warke," in ji Dakta.

Comments