Hanya biyu daza a bi don Kara Qiba ga Macen da takeso tadan cicciko daga rama.
(1) Domin Karin kiba Za'a samo Zabib,da hulba, Za'a wanke Zabib din sannan azuba shi acikin ruwa Kofi biyu, sai shi yayi awa (16) Sannan a murtsike shi a tace bayan ya hade sai kuma a zuba hulba cokali (2) idan ruwan yayi kasa Sai a kara wani daga nan sai asanya a frigde a rufe amma banda marfin Wanda zai rufe kwanon ko robar gamgam. Idan yakara kamar awa (6) Sai a tace za'arika shan karamin kofin shayin larabawa ko buzaye.
Sai dai yakan sanya kara cin abinci, to ana bukatar a rika cin abinci mai kyau wanda yake gina jiki.
Hadi na biyu Kuma, za a samo zabib Kofi biyu, a wanke sosai sannan a zuba a ruwa a kalla kamar Rabin Lita zuwa Lita daya sannan a zuba garin hulba mai kyau Kofi daya sai a zuba a kalla zaiyi awa 12-18 ko dare cikakke daganan za a tace a zuba a waje mai kyau sai a rika shan karamin Kofi sau 3-4 arana.
Sannan sai a rikacin kwaya goma sau 3 a rana insha Allah za ayi wannan hadin sau 2-3 ya isa, insha Allah za ayi mamaki sosai, wannan anjarraba angwada kuma antabbatar.
Sannan cin zabib yana magance sihir da kuma matsalar shaidanun aljannu, cinsa kuma yakan zama asamu kariya daga sihir, ko shafar jinnu.
Comments
Post a Comment