Hanyoyi goma da Mace zata bi don magance kurajen fuska, musamman gyaran fuskar Amarya
Amare da dama suna fama da matsalar kurajen fuska musamman farar mace Wanda sune sukafi fuskantar wannan matsalar.
Zanyi bayanin hanyoyi goma Wanda amarya zatabi don magance matsalar kurajen fuska
(1) Da farko ana so awa biyu ko uku kafin ki kwanta barci sai ki shafa man goge baki a fuskarki, musamman wuraren da kurajen pimples suke da yawa. Ba kowane irin man goge baki za ki shafa ba, ana so ki shafa farin man goge baki ne. Idan kin ga dama za ki iya wanke fuskarki idan man goge bakin da kika shafa ya kai minti 30, idan kin ga dama kuma za ki iya kwantawa da shi har zuwa wayewar gari. Za ki rika maimata hakan har zuwa wadansu kwanaki, idan kin yi hakan za ki ga canji a fuskarki Insha Allah.
(2) Ki kasance mai yawan shan ruwa.yawaita shan ruwa ba wai zai sanya miki laushin fata ba ne kawai, a’a, zai taimaka miki wajen yaki da kurajen pimples din da suke fuskarki. Haka yana da kyau ki guji yawan cin abincin gwangwani, kasancewar suna dauke da wasu sinadarai da zasu rika sanya kurajen fuska. Ya kamata ki yawaita cin ‘ya’yan itatuwa da suka hada da su abarba da lemu da ayaba da kankana da sauransu.
(3) Ki rika amfani da abin shafawar da ake kira ‘(Antioxidant spray) irin su (Jane Iradale) da (Neutrogenia Rapid Clear) da (Acne Eliminating Spot Gel) da sauransu, hakan zai taimaka miki wajen daidaita man da ke fatarki, wanda masana fata suka ce idan yayi yawa yakan haifar da kurajen fuska.
(4) Ki kasance mai amfani da man (Cornmeal) a fuskarki, yakan sanya kurajen fuska su motse sannan a hankali su bace, misali man shi ne; (Intagilo Clear Sal Cleanser.) Sannan kirika amfani da man da ke hana yaduwar kwayar cutar bakteriya, irin wannan man yakan ratsa kofofin da suke fatar fuskarki da ma jikinki gaba daya, sannan yana yakar kwayoyin cutar da suke fatarki, a lokaci guda ya daidaita miki yawan man da yake fitowa daga fatarki. Zai kuma cire miki kwayoyin halittar da suka mutu a cikin fatarki. Misalinsu; (Phytomer Gommage) da Luffa-0.
(5) Yana da kyau ki ware wata rana ko wadansu ranaku a cikin mako batare da kin shafa kayan kwalliya a fuskarki ba, hakan zai bai wa fatar fuskarki samun ‘yancin shigar da kuma fitar da iska ta kofofinta ba tare da wani cikas ba. Haka idan za ki shafa kayan kwalliyar a fuskarki, to kiyi amfani da kayan kwalliyar da basa toshe kofofin fatar fuska.
(6) Ki kasance mai shafa mai domin fatar fuskarki ta kasance cikin danshi, kasancewar wadansu kurajen fuskar sun fi bata fuska idan fuska tana bushe.
(7) Yi amfani da man (Tea Tree’)domin ba wai kawai yana baje kurajen fuska ba ne, a’a yana rage karfinsu da kuma kalarsu. Za ki sami ire-iren wadannan man a shagunan sayar da kayan kwalliya na zamani.
(8) Ki kasance mai yin taka tsan-tsan wajen amfani da ire-iren man shafawar da kike amfani da su agashin kanki, ma’ana kada ki sake yarika taba fuskarki hakan zai iya haifar miki da kurajen fuska, kasancewar wadansu sinadaran an yi su don su taimaka wa gashin kai ne, don haka idan suka shiga kofofin fatar fuskarki, sai su haifar miki da matsala.
(9) Ki kasance mai gasa kurajen fuskarki: Duk lokacin da kurajen pimples suka fito miki sai ki samu wani kyalle mai tsafta, sai ki tsoma shi a ruwan zafi, ba wanda ya tafasa ba, bayan kin tsoma sai ki fito da shi, sai ki rika dora shi a kan wajen da kurajen suke, sannan ki rika gogawa a hankali, zafin kyallen yakan sa kurajen su motse daga nan su mutu.
(10) Ki guje yin amfani da hannun kiwajen fasa kurajen da suke fuskarki, domin hakan yana kara yawansu hade da sanya fuskarki ta kara cabewa.
Comments
Post a Comment