Main menu

Pages

ILLOLIN KWANA DA GARWASHI KO RUSHI A CIKIN DAKI LOKACIN SANYI

 



Illolin da kwana da garwashi a lokacin sanyi ke haifarwa, ga Lafiya da jikin Mutum


A yayin da ake ƙara shiga sanyi, masana a fannin lafiya a Najeriya sun gargaɗi alumma da su kauce wa kwana da garwashin wuta saboda illolin da yake da shi ga lafiya.


Masanan dai sun ce kwana da garwashin wutar kan haifar da wasu cututtuka da ke shafar numfashi, da illa ga fatar jikin dan Adam.


Gargaɗin likitocin na zuwa ne a dai-dai lokacin da aka samu wasu ma'aurata da ake zargin sun rasa ransu sakamakon kwana da irin wannan garwashi a daki yankin Ƙarmar hukumar Dawakin Tofa a Kano.


A irin wannan lokaci na sanyi, akan saka garwashin a ɗaki domin ya yi ɗumi. Sai dai kwararru na cewa hada wuta sasakai a daki yana da matukar hadari.




A cewar Dr. Hadiza Ashiru likitar yara a Najeriya, ta ce kwana da gwarwashi kan haifar da cututka.


"Abu na farko da yake haifarwa shi ne gobara, da kan haifar da asarar dukiya a wasu lokuta har ta kai ga rasa rai," in ji Dakta Hadiza Ashiru.




Hakazalika Dakta Hadiza ta ce hayaƙin da garwashin ke fitarwa, duk da ba shi da wari, yana zama illa idan aka ajiye shi a ɗaki saboda sinadarin nau'in carbon mono oxide wanda yake dauke da guba, da zai iya illata huhun mutum, wanda hakan ke haifar da cutar kansa.




"Yana haifar da matsalar numfashi, da ƙona hanyoyin da iska ke bi, sannan yana da illoli sosai ga masu cutuka da suka shafi numfashi irin su Asma, da ke halaka su cikin dare da wasu lokutan akan wayi gari sun mutu."




Har ila yau Dr. Hadiza Ashirun ta ce hayaƙin da garwashin ke fitarwa na da illa ga fatar mutum, da yiwuwar cutar mantuwa, da ta ƙwaƙwalwa idan mutum ya fara tsufa.




Sai dai ta ce barin tagogin ɗaki a bude, da sanya garwashin ya dumama ɗakin kafin a kwanta shi ya fi kamata saɓanin kwana da garwashin.



Sannan ta ja hankalin al'umma da su kwana da rigar sanyi, da safa, da bargo mai kauri, idan za a kwanta, idan an sami tsananin sanyi mai yawa

Comments