Main menu

Pages

ILLOLIN YIN FAMILY PLANNING GA MACE MAI KANANUN SHEKARU

 



Illoli da cutarwan yin Family Planning ga Mace Mai kananun shekaru. Da ire - iren planing da muke dasu.


Manufar mu a Kullum Itace Wayar da Kan Al'umma, da bada taimako akan ko Wace irin matsala ta rayuwa bisa koyarwa ta addinin musulunci 



Wannan babban hatsarine kaga mace me shekarun da Basu wuce 23 zuwa 24 ba Kuma Bata wuce haihuwa 1 zuwa 2 ba har ma da masu sabon Aure Zaka ga har da su suna da Sha'awar yin family planning ta hanyar Shan kwayoyi kokuma yin allura ko saka roba.




Kuma dayawa ana yin aikin ne ba tare da anbi ka'idojin yin family planning na addini ko na Asibiti ba



Wannan babban hatsarine yana illata mahaifar mace musamman ga wadda Bata taba yin haihuwa ko 1 ba illace da takan hana haihuwa kwata kwata da maida Mace infertility.




Acikin rukunnan planning akwai su kamar haka:

1. Depo provera: wannan alurace da mata su kan yi domin samun tsaikon haihuwa na wata (3) Wanda kafin yinta a tabbatar da mace tana da haihuwa kusan (3 ko 4) zuwa sama. Saboda allurace me matukar hatsari da lalata mahaifa da canzawar Al'ada ga "ya mace, wanna alurar ba a yiwa mace me haihuwa 1 ko 2 zuwa 3 sedai wadda tai haihuwa kamar 4 zuwa sama.




2. Noristerat; Wannan itama allurace  da ake yiwa Mace tazarar haihuwa na wata 2 wadda ita ana yima masu kananan haihuwa kama daga haihuwa 1 ko 2 wannan a cikin allura tana da saukin Sha'anibisa ga (depo provera) ta wata 3



3. Pills; Shan kwayoyin planning Shima yana da kalar tasa illar na sanya Mace zubar jini ko ba a lokacin (period) ba sannan Shima yana hana haihuwa kwata - kwata ga wasu Matan.




4. Implanum; Robar hannu ko Ashanar Hannu wanan itace ake sakama Mata a hannu ta shekaru kamar 4 zuwa 5 wanan itama illarta mussaman ga wadda bata taba yin haihuwa ba takan hana haihuwa da Kuma sanya mace tayi kiba kokuma tayi rama tana kuma sanya zubar jini Idan zubar jini yayi yawa to anemi likita.




5. I.U.D; wannan planning ne da ake sakama Mace a mahaifa cikin farjinta Shima yana da irin nashi matsalar. Amma tun shigowar implanum yawanci anfi yin amfani da ita fiye da I.U.D din.

Comments