Ku labubi lokuttan karbar addu'a na Ranar Juna'ah tsadaddiyar sa'a ce ta Dan lokaci
Shaykh Ibnu Baaz(RA) ya ce:
Ubangiji ya sanya wata sa'a a ranar juma'a wanda ya ke karban addu'a a cikinta, lokaci ne kadan wanda babu wani musulmi da zai dace da ita yana tsaye yana sallah face Allah ya bashi abin da ya roka, don haka lokaci ce mai girma kuma bata da tsawo.
1-Ya zo a wasu riwayoyin cewa lokacin shine sanda liman ya zauna a kan minbari zuwa a idar da sallah.
2-Ya zo kuma cewa lokacin yana a tsakanin Sallar La'asar zuwa faduwar rana.
3-Ya zo a wasu hadisan cewa lokacin shine sa'ar karshe na ranar juma'a
Wadannan sune lokutan da a ka fi tsammanin wannan sa'a, haka sauran lokutan juma'a gaba daya a na fatan a amsa addua cikinsu.
Don haka ya kamata musulmi ya yawaita addu'oi a ranar juma'a don fatan dacewa da wannan sa'ar, kuma ya kamata ya ribaci wadancan lokuta ukun da a ka ambata a sama ya ba su karin kulawa domin Manzon Allah(SAW) ya nafsanta cewa shine lokacin amsar addu'a.
Allah Ya sa mu dace da Wannan lokaci.
Comments
Post a Comment