Manya - Manyan Kurakuran da Ma'aurata ke takawa ba tare da sun sani ba.
Aure na iya zama abu mafi kololuwar jin dadi da walwala a rayuwar dan Adam, a wasu lokuttan kuma ya kan zama tamkar mutum na zaune a gidan yari ne wani sa'ilin ma na gidan yari yafi ka kwanciyar hankali. Hakan duk ya ta'allaka ne da waye ka aura.
A wannan zamani da mu ke ciki, aure ya zama abinda ya zama a Arewa. Yawaitar mutuwar aure kullum kara yawa ya ke. Har ta kai ana iya aure wata daya a rabu.
Akwai abubuwa masu dadi a rayuwar aure, musamman ka tuna cewa wannan na zaba a matsayin aboki ko abokiyar rayuwata. Sannan akwai kalubale da ke fuskantar aure wanda sai an taru gaba daya wajen tunkarar sa.
Da yawa a tunanin su rayuwar aure, rayuwa ce ta jin dadi da more rayuwa na dindindin, sai dai bayan shigar su sai su iske abun ba haka bane.
Masana sun nuna cewa rayuwar aure gaba dayanta wata makaranta ce mai zaman kanta, ba wai makarantar je ka ka dawo ba, a'a makaranta ce da ba'a fita cikinta.
Akwai kura-kurai da ma'aurata kan aikata wadanda ke jawo matsaloli a rayuwar aure, wanda wasu basu dauke su a bakin komai ba, daga karshe kuma kan iya jawo mutuwar aure.
1- Daukar juna ba a bakin komai ba
Da yawan ma'aurata ganin an kwana biyu tare, an saba da juna sai ya zama kar ta san kar ne, su kan manta da abubuwan da kan kara ma zamantakewar su armashi.
Zai zamo mace duk abinda mijinta zai yi ba za ta ga bajintar shi ba, tana ganin ai dolen shine dan haka ba ta ga abin yabawa ba. Haka ta bangaren maza ma, babu wannan yabawar tsakaninsu da matansu.
Yana da kyau komin kankantar abu da miji ko mata ta/ya yi, a yaba a kuma gode. Hakan zai kara karfafawa mutum. Idan girki tayi, kamata yayi ka gode ma ta, tare da kwarzanta abincinta, haka bangaren kwalliya ma. Shiyasa wasu matan da sunyi aure, duk wata kwalliya sai su zubar saboda mazajensu ba sa yabawa.
Haka ta bangaren hidimar gida, ya kamata mata su rika yabawa mazajensu duk da cewa hakkinsu ne su dauki nauyin iyalansu, amma yana da kyau a gode mu su. Hakan zai kara mu su karfin gwiwa.
2- Dogon buri
Da yawan maza da mata kan shiga gidajen auren su da dogon buri, suna tunanin babu komai a cikin rayuwar aure face jin dadi. Sun dauka irin rayuwar fina-finai ce da abubuwa na jin dadi da suke gani. Sai dai kash, rayuwa ce mai tattare da kalubale, wata rana zuma wata rana madaci.
Dogon burin da ake shiga da shi na daga cikin manyan kura-kurai da ma'aurata ke tafkawa. Sai bayan an shiga a ga akasin abinda ake tsammani, wanda wasu idan an yi sa'a su kan yi hakuri da abinda suka iske, wasu kuwa a lokacin ne fitintinu za su yi ta bullowa.
Ya zama wajibi ga ma'aurata su cire dogon buri a rayuwar aurensu, su rungumi abinda suka tarar da hannu biyu da yaƙinin cewa canji na faruwa ne daga kan mutum, sannan daya ya yi adapting da canjin.
Kasancewar aboki ko abokiyar rayuwar da wani nakasu a rayuwa ba shi ke nuna cewa rayuwar zamantakewa ta ruguje ba. Kowane dan adam tara yake bai cika goma ba. Haka kowane rayuwar aure bai cika dari bisa dari ba, dole a samu tawaya ta wani bangaren.
3 - Rashin hakuri
Gaba daya rayuwar aure yar hakuri ce, sannan hakuri shine ribar zaman duniya.
Muna cikin wani zamani da ma'aurata kamar jiran juna su ke, kowane a wuya yake danuwarsa ya yi abu ya zama abin fada da cece-kuce.
Kowane ma'aurata suna samun sabani a tsakanin junansu, sai dai mi? Wasu kan yi kokari wajen ganin sun gano bakin zare ta hanyar warware matsalolinsu ta hanyar lumana.
Wasu kuwa a lokacin ne zage-zage, buge-buge da bakaken maganganu ke kunno kai. Daga nan sai wutar ta kara ruruwa, har ta kai ga abinda ba a so.
Wasu ma'auratan koda su ne da laifi ya kan zama abu mai matukar wahala su bude baki su bada hakuri. Daga nan sai gardama ta biyo baya. Ko dan zaman lafiya bada hakuri na kashe wutar fitina.
4- Mantawa da yanda za a so juna
Daga zarar anyi aure, duk soyayyar da aka tafka a baya sai ta zama tarihi. Babu sauran soyayya da an yi aure komai ya zama tarihi.
Comments
Post a Comment