Wasu muhimman shawarwari guda biyar Zuwa ga Amaryar Gobe. Abubuwan da ya kamata tayi da Wanda zata kiyaye.
1. Tun da dai ke budurwace baki taba aure ba, to ki guji duk wasu kayan da’a ko hakkin maye da za a ba ki don ki sha, domin tun asali irin wadannan magunguna an yi su ne don matan da suka dan jima cikin aure kuma zuumar sha’awarsu ta dan fara sanyi.
Wadanda ba su taba aure ba kuwa zuumarsu na nan da zafinta, don haka babu wani dalili na zukakata da irin sinadaran zukakawa; wannan ke sa nan gaba a samu rikirkicewar sha’awa domin yamutsa ta din da aka yi da wadannan sinadarai maimakon a bar ta ta tafiyar da kanta a kan irin tsarin da Allah Ya tsara mata.
2. Amma kina iya shan ‘ya’yan itatuwa da yawa gab da bikin naki, inda hali ma, kina iya daina cin duk wani abinci illa ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki kadai kamar ana sauran sati daya bikin naki.
3. Haka ma magungunan Musulunci da ka samu ingancin warakarsu daga Manzon Allah SAW, irin su zuma, habbatus sauda, zaitun da sauransu. Wadannan za su warkar miki da duk wani rauni ko cikas da kila kina da shi a lafiyar jikinki da ta ruhinki gaba daya.
4. Sai kuma ki rika yawan shan ruwa, a kalla ki sha kofi takwas na ruwa kullum.
5. Sannan ki tsabtace zuciyarki da kyawawan shau’uka da tunani da kyautata zato da fatan alheri. Allah Ya ba ku zaman lafiya tare da sauran dukkan ma’aurata Musulmi, amin.
Comments
Post a Comment